Yadda Ake Tafiya Sujudah

0
541

Tafiya Sujudah: Akwai hadisin da ya ce mai sallah ya fara ajiye gwuiwarsa kafin hannayensa. Ruwayar (wa’il ibnu hujur).

Akwai kuma hadisin da ya ce ; ya fara ajiye hannayensa kafin gwuiwarsa, ruwayar (Abu Huraira); shi ne wasu malaman suka ce; gwuiwar raƙumi a hannunsa take saboda haka, da hannuwanka za ka tafi ba da gwuiwa ba.

Wasu malaman kuma suka ce; ruwayar (Wa’il ibnu Hujur) ita ce ta zo daidai ruwayar (Abu Huraira); ta zo a baibai ne, saboda haka da gwuiwar ƙafafunsa zai tafi sujuda ba da hannuwansa ba.

Domin karanta cikakken bayani a kan Abin Da Ya Kamata Mai Yin Sallah Ya yi Bayan Ya Tafi Sujudah danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Sallar Roƙon Ruwa danna nan.

labarin da ya wuceYadda Ake Dawo Da Abin Da Aka Goge A Kan Komfiyuta
Labarin na GabaHidisai Goma Kan Hatsarin Shugabanci
Lawan Bello
Abu muzaffar Malami ne masanin ilimin zamani da na addini bisa tsaren Ƙur'ani da tafarkin manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, mai hangen nisa a addini da kuma alummma, shugaban Abu Muzaffar foundation.