Tag: Falalar

  • Hadisi Na Bakwai Akan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

    Hadisi Na Bakwai Akan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

    An karɓo daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Asi (Radiyallahu Ahuma) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Haƙiƙa masu adalci za su kasance a kan mimbarai na haske a daman Allah mai rahama, kuma duk hannayensa biyu dama ne. Su ne waɗanda suke yin adalci a cikin hukuncinsu da iyalansu da waɗanda suke jagoranta.

    Muslim da Nasa’i ne suka rawaito shi.

    ƘARIN BAYANI

    Haƙiƙa masu yin adalci da gaskiya a shugabancin da yake kansu da iyalansu suke kaucewa zalunci da nuna bambancin a tsakanin waɗanda suke jagoranta, za su samu babban matsayi a wurin Allah ranar lahira.

    Hannun dama da ya zo a wannan hadisin sifa ce daga sifofin Allah Ta’ala waɗanda ake yin imani da su kamar yadda suka zo, ba tare da an yi musu tawali ko canja su ko kore su ba ko kuma kamanta su da sifofin halittu ba.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Hadisi Na Takwas Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu A kan Shugabanci) wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Hadisi Na Uku A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

    Hadisi Na Uku A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

    An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) ya ce: Na ji mai gaskiya abin gasgatawa mai wannan ɗakin baban Alƙasim (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: “Ba a cire tausayi sai daga zuciyar mara rabo a lahira”.

    Abu Dawud da Tirmizi ne suka rawaito shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Hadisi Na Huɗu A kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu Akan Shugabanci) wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Yadda Falalar Karatun Al-Ƙur’ani Ya Ke

    Yadda Falalar Karatun Al-Ƙur’ani Ya Ke

    Karatun ƙur’ani ibada ce babba wacce babu sama da ita; musamman in ta haɗu da ikhlasi da lura da ma’anoni da manufofin abinda ake karantawa (Tadabbur) da karantawa dai-dai da ƙa’idodin karatun (Tajwidi); da kuma abinda ya fi komai muhimmanci wato aiki da abinda ake karantawa.

    Hadisai da dama sun zo kan bayanin Falalar Karatun Al-Ƙur’ani a jumlace; da kuma falalar karanta waɗansu keɓaɓɓun surori da ayoyi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Koyo Da Koyarwar Da Al-Ƙur’ani Ya Ke danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Zikiri danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Falalar Sadaƙar Mai Ƙaramin Ƙarfi

    Falalar Sadaƙar Mai Ƙaramin Ƙarfi

    An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu anhu) ya ce: “Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) yace: “Sadaƙar dirhami ɗaya ta rigayi sadaƙar dirhami dubu ɗari” Sai wani mutum ya ce; Kamar yaya Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam)?

    Sai ya ce: “Mutum ne yana da dukiya mai yawan gaske, sai ya tsakuro dubu ɗari ya bayar sadaƙa; kuma wani dirhami biyu ne kaɗai da shi. Sannan ya yi sadaƙa da dirhami ɗaya” (Nasa’I Ibn Khuzaimah), (Sahihul Targib 875).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Ciyarwa Da Shayarwa Da Tufatarwa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ratiban Nafiloli danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Falalar Biyawa Wani Hajji Ko Umra

    Falalar Biyawa Wani Hajji Ko Umra

    Haƙiƙa duk wanda ya kasancce sanadin aikata alhairi, za a ba shi lada dai-dai da ladan wanda ya aikata wannan aikin ba tare da an rage komai daga ladansa ba..

    A kan haka, wanda ya biyawa wani kuɗin aikin hajji ko Umra; za a ba shi lada da za a baiwa wanda ya yi aikata aikin hajji ko umra. Saboda haka, magabata suka kasance suna ɗaukar nayin waɗanda ba su taɓa yin aikin hajji ko umra ba.

    Misalin Waɗannan magabata akwai Muslim Ibn Yasar da Abdullahi Ibnul Mubarak; waɗanda suka kasance suna aikin hajji duk shekara, kuma suna tafiya da mutane da suke ɗaukar nauyinsu!.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Karatun Al-Ƙur’ani Ya Ke danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Karatun Al- Kur’ani

    Falalar Karatun Al- Kur’ani

    An karɓo daga Abu Umamah (Radiyallahu Anhu) ya ce: Na ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: “Ku karanta Alƙur’ani saboda haƙiƙa zai zo rana alƙiyama zai ceci ma’abotansa.” (Muslim: 804) 

    An karɓo daga Abdullahi Ibn Amr As (Radiyallahu Anhu) yace: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Wanda ya karanta harafi daga littafin Allah, Za a ba shi kyakkyawan (Lada) ga kowane harafi, za a kuma ninka kowane lada sau goma. Ba ina cewa Alif lam mim harafi ɗaya ke nan ba, a’a Alif harafi ɗaya, Lam harafi ɗaya, Mimun harafi ɗaya”.(Tirmizi: Sahihul Jami’i 6469).

    FALALAR FATIHA 

    An karɓo daga Abu Sa’id Ibnul Mu’alla (Radiyallahu Anhu) yace: Na kasance ina salla a masallaci sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kira ni. Sai ban amsa ba, sanna sai na je wajensa na ce salla nake yi. Sai ya ce: “Shin Allah bai ce: ” Ku amsawa Allah da Manzonsa ba idan suka kira ku? 

    Domin karanta bayani akan Falalar Kuka Ranar Ashura Danna nan 

    Sai ya ce: zan sanar da kai surar da ta fi kowace saura girma a cikin Alƙur’ani kafin ka fita daga masallaci”. “Sai ya riƙe hannuna, da muka kusa fita sai na ce: “Ka ce za ka sanar da ni saurar da ta fi kowace sura girma a cikin Alƙur’ani, sai ya ce:”Ita ce Alhamdu lillahhi rabbil alamin; Ita ce(Mai ayoyi) bakwai da maimaitawa kuma itace Alƙur’ani, mai girma da aka ba ni” (Bukahri: 4202). 

    FALALAR SURATUL BAƘARA 

    An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “kada ku mayar da gidajenku kamar maƙabarta, Haƙiƙa Shaiɗan yana gudu daga gidan da ake karanta Suratul Baƙara a cikinsa”. (Muslim 708). 

    An karɓo daga Abu Umamah (Radiyallahu Anhu) haƙiƙa ya ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: “ku riƙa karanta suratul Baƙara saboda riƙo da ita albarka ne, barinta nadama ne, kuma matsafa basa iyawa da ita”. 

    (Muslim 804) Wato karanta suratul baƙara yana maganin sihiri da tsafi da kuma sharrin shaiɗanu. 

    Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

    FALALAR KARANTA AYATUL KURSIYYU 

    An karɓo daga Ubayyu ɗan ka’ab (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ya baban Munzir, Shin ka san wacce aya ce mafi girma a cikin Al-ƙur’ani? Sai na ce: Allahu laa ilaha illa huwaL hayyul ƙayyum” ya ce: Sai ya bugi ƙirji na ya ce:

    Ina taya ka murnar ilimi, ya baban Munzir (Wato yana taya shi murnar sanin hakan). 

    FALALAR KARANTA AMANAR RASULU 

    An karɓo daga abu Mas’ud Albadri (Radiyallahu Anhu) haƙiƙa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce “Wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshen Baƙara a cikin dare sun isar masa” (Bukhari: 3786, muslim 807). 

    Malamai sun bayyana ma’anar “sun isar masa” da cewa za su zama garkuwa a gareshi daga dukkan sharri, ko kuma za su tsaya a masa a matsayin ƙiyamul laili”. 

    FALALAR AYOYI GOMA NA FARKON KO ƘARSHEN SURATUL KAHFI 

    An karɓo daga Abu Darda’i (Radiyallahu Anhu)Haƙiƙa Annabin Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Wanda ya haddace ayoyi goma na farkon Suratul Kahafi, za a kare shi daga Dujal” (Muslim 809) A wata ruwayar ayoyi goma na Ƙarshen suratul kahfi. 

    FALALAR TABARAKALLAZI BIYADIHIL MULKU 

    An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: haƙiƙa wata sura a cikin Alƙur’ani mai ayoyi talatin ta ceci wani mutum har sai da aka gafarta masa, ita ce: “Tabarakallazi biyadihil mulku” (Abu Dawud, Tirmizi, Nisa’I Ibn Majah, Sahihul Jami’i 2091). 

    FALALAR ƘULHUWALLAHU AHAD 

    An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) yace: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: ” Ku taru zan karanta muku ɗaya bisa ukun al-ƙur’ani, sai waɗanda suka haɗu suka haɗu, Sai Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya fito sai ya karanta “ƙulhuwallahu Ahad”.

    Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

    Sannan ya shiga gida, sai muka ce da junanmu muna zaton wahayi ne ya zo masa daga sama, shi ya sa ya shiga gida, sai ya fito ya ce haƙiƙa na ce da ku zan karanta muku ɗaya bisa ukun al-ƙur’ani, ku faɗaka haƙika ita (ƙulhuwallahu tana daidai da ɗaya bisa ukun al-ƙur’ani”. (Muslim 812). 

    FALALAR FALAƘI DA NASI 

    An karɓo daga Uƙubatu ɗan Amir (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ba ka ga waɗansu ayoyin da aka saukar da su jiya da daddare ba, ba a taɓa ganin irinsu ba”. Sune ƙul’a’ uzu bi rabbiL falaƙi” da ƙul’a’uzu birabbinnasi” (Muslim 814). 

    FAƊAKARWA 

    Ina nasiha da ba da shawara ga ‘yan uwa musulmi da mu kula sosai da Alƙur’ani ta wajen haddace shi, da yawan karanta shi, da koƙarin fahimtar ma’anonisa da kuma yin aiki da shi domin samun tsira da arziki da wadata a duniya da lahira. 

    Allah ka sa mu dace, Allah ka sanya mu zama ahalinka a halin Alƙur’ani. Amin.

    Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

  • Falalar I’itikafi

    Falalar I’itikafi

    I’itikafi shi ne tarewa a masallaci domin yin ibada. Ana son yin I’itikafi a kwanaki goma na ƙarshen Ramadan, kamar yadda Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) ya kasance yana yin ittikafi har Allah ya karɓi ransa.

    An karɓo daga A’isha (Radiyallahu anha) ta ce: Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) ya kasance yana i’itikafi a goman ƙarshe na Ramadan har Allah ya karɓi ransa. iyalansa ma sun yi i’itikafi bayan wafatinsa. (Bukahri 2026 Muslim 1172).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Raya Daren Lailatul Kadari danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Gaggauta Buɗa Baki

    Falalar Gaggauta Buɗa Baki

    An karɓo daga Sahal Ibn Sa’ad (Radiyallahu anhu) Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce:

    “Mutane ba za su gushe ba a kan alhairi mutuƙar suna gaggauta buɗa baki”. (Bukhari 1957 Muslim 1098).
    Kuma an ruwaito daga shi (Sahal) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce:”Al’ummata ba za su gushe ba a kan sunnata, matuƙar ba sa jiran fitowar taurari kafin su yi buɗa baki”. (Ibn Hibban 1957, Sahihut Targib 1074).
    Waɗannan hadisai suna nuna cewa, jinkirin buɗa baki har sai an yi sallar magariba, ko har sai taurari sun fito bidi’a ne, kuma ɗabi’ar Yahudu da Nasara ce, kamar yadda ya tabbata a hadisin (Ibn Hibban 3562).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Yin Sahur danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Azumin Tasu’a Da Ashura

    Falalar Azumin Tasu’a Da Ashura

    An karɓo daga Ibn Abbas (Radiyallahu anhu) yace; “Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya yi Azumin Ashura, kuma ya yi umarni a yi sai (sahabbai) suka ce:

    “Ya Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) wannan rana ce da Yahudawa ko Kiristoci suke girmamawa, sai ya ce, “Shekara mai zuwa insha Allahu zan fara da azumin ranar tara (tasu’a) kafin shekarar ta kewayo, Allah ya karɓi ransa”. (Muslim 1134).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yawaita Azumi A Watan Sha’aban danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Nafilolin Azumi

    Falalar Nafilolin Azumi

    Kamar sallah, shi ma azumi yana da nafiloli waɗanda ya kamata musulmi ya kula da su domin samun kusanci ga Allah maɗaukakin Sarki, ga taƙaitaccen bayani kan ingantattu daga cikinsu.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Azumin Watan Muharram danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.