Hani Akan Yin Duba 2

0
39

Ilimin “Geomancy” shi ake kira da “ramli” ko kuma duba akan yashi (har da biro da takarda duk ana yi). Ilimi ne da ya fita daga rubutaccen ilimin taurari (Astrology), don haka yake da sunaye da kuma salon bincike kusan iri ɗaya da na ilimin taurarin kuma an fi kyautata zaton larabawa su ne suka fara yin sa har ya watsu zuwa ƙasashen Africa da Europe.

Shi ilimin ramli ɗigo-ɗigo a ke yi kusan kala 14 don a fitar da waɗansu abubuwa daga jikin ɗigon. Wanda na koya ina shekara 13 yana aiki ne da zanen da ya fito bayan ka gama zanen da ba ka ƙirga ba kuma ka soke biyu-biyu daga cikinsa. Idan 1 ta fito to za a auna ta da dai-dai buƙatarka, haka ma idan biyu ta fito. Akwai ababan mamaki a cikin ilimin da suke faruwa amma dai shi ma ana ɗora su ne kamar yadda ake ɗora sauran iliman Astrology.

Akwai ababan mamaki da suke faruwa a cikin irin waɗannan iliman waɗanda har yanzu kimiyya ta kasa gano ya haƙiƙarsa take. Waɗansu abubuwan kamar “Telepathy”, “Entanglement”, “PSI” da sauransu har yanzu suna ba wa masu kimiyya mamaki duk da suna ɗora su a babin “Pseudosciences”.

Yadda aka iya gano “Kuantum entanglement” to ana zaton za a iya fahimtar waɗansu abubuwan irin waɗannan da tafiyar lokaci. Zamanin amfani da “Classical Physics” na Newton da ya ɗoru akan lissafin Euclid ya wuce. Yanzu muna kan “Kuantum Mechanics” wanda ƙaryata abu ta farar ɗaya, don dogaro da kimiyya (classical physics) na nuna raunin mutum a sanin kimiyyar.

Ana buƙatar bincike na sosai akan abu kafin a ƙaryata shi. Yanzu muna kan “super string theory” wanda ya ce duniya tana da “10-dimensions” maimakon 3-dimensions ko 4-dimensions da Einstein ya kawo! Hankali zai ruɗe bai gano haƙiƙar abubuwa masu “10-dimensions” ba amma hakan baya nufin cewa “super string” ƙarya ne don kawai ba ka fahimci yadda yake ba.

Abu Hamidil Gazhali, a cikin “Almunkidh” yana magana akan “secrets of numbers”, yana faɗin cewa akwai abubuwan mamaki a cikin waɗansu lambobin. Ya ba da hoton waɗansu lambobi da ya ce an kasa gane sirrinsu. Lambobi ne kawai a jere amma idan aka haskawa mai ciki a lokacin da take naƙuda sai a ga ba ta shan wahala sosai!

Ibn Khaldun ya faɗi waɗansu lafuza da yaren “Armenians” inda ya ce in dai ya karanta su to sai ya yi mafarkin abin da yake so! Abubuwan da ban mamaki ta yadda ake buƙatar a yi zurfaffen bincike a kai. Irin wannan to da su aka ɗora iliman “Numerology” da karanta zanen hannun mutum ko ƙirgen da a ke yi da carbi.

Danna nan don karanta Hani Akan Yin Duba 1

Edita; Rumasa’u M. Kallamu

labarin da ya wuceHani Akan Yin Duba 1
Labarin na GabaMe Ke Kawo Warin Jiki?