Kamannin Annabi Muhammad (S.A.W), Kyan Halittarsa Da Siffarsa

0
24

Abu ne mai matuƙar muhimmaci ga musulmi ya san kamannin Annabi Muhammad (S.A.W) da siffarsa. Domin abin da mutum yake so ya kamata ya san shi. Kuma ma ai mukan ce: “Allah ya sa mu ga Annabi” watau a Lahira. Kai ba ma sai a Lahira ba. 

Babu shakka ganin Annabi Muhammad (S.A.W) a mafarki abu ne mai yiwuwa. Amma yaya za a yi mutum ya san shi kuma ya gan shi? Babu shakka sai mutum ya san kamanninsa sannan zai san shi ɗin ya gani a mafarki. Ga dai yadda lamarin yake a hadisin Abu Huraira (R.A): 

“Daga Abu Huraira (R.A) ya ce: “Na ji Annabi Muhammad (S.A.W) yana cewa: “Wanda duk ya ganni a mafarki, to zai gan ni a farke. Shaiɗan ba ya kamantuwa da ni”, (Bukhari da Muslim suka ruwaito). Imamul Bukhari ya ce: Malam Ibnu Sirina1 ya ƙara da bayanin cewa: “Idan ya gan shi a kamanninsa”. Ka ga ke nan dole sai mutum ya san kamanninsa. Idan ba haka ba, sai Shaiɗan ya zo wa mutum a kamar da ba ta Annabi ba. 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

A wata ruwayar ta Muslim: “Wanda ya gan ni a mafarki to zai gan ni a farke, ko kamar ya gan ni ne a farke. Shaiɗan ba ya kamantuwa da ni”. 

Wannan ya nuna cewa, lallai ne duk musulmi ya san kamannin Annabi Muhammad (S.A.W). Malamai sun yi ƙarin bayani game da jimlar: (To da sannu zai gan ni a farke), inda suka ce, “Wannan jimilar ta zo a ɗayan ruwayoyin Muslim tare da nuna shakka daga mai ruwaya kan ɗayan biyu: Watau da ƙari kamar haka: “Ko kamar ya gan ni a farke”. 

1Shi ne Muhammadu bin Sirina. Babban tabi’i, mutumin Basara. Malamin Tafsiri da Hadisi da Fiƙhu, Ya rasu a shekarar hijra ta: 110 yana da shekaru sama da tamanin, bayan rasuwar Hasnul Basari da kwana ɗari.

Haka kuma ya zo a wata ruwaya kamar haka (haƙiƙa ya gan ni a farke)2. Watau, “Ni ya gani, gani na haƙiƙa”3 

Abin nufi a nan shi ne, kada ka wahalar da kanka da fassarar masu cewa idan mutun ya gan shi a mafarki to zai gan shi a duniya, kuma a farke. Wannan ɓatacciyar fassara ce. 

Ba ta da tushe a addini. Abin da za ka fahimta shi ne, sauran ruwayoyin biyu ƙarfafa ganin suka yi. Wannan ya sa malamai suka ɗauka ta farkon ma haka take nufi watau ƙarfafa ganin take nufi. Ba wai tana nufin za a gan shi a farke a wannan duniyar tamu ba. 

SIFFAR JIKIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W): 

Allah (SWT) ya fifita Manzonsa da kyan halitta, fiye da sauran bayinsa. Annabi Muhammad (S.AW) mutum ne madaidaicin halitta. Ba dogo ba, ba kuma gajere ba. Watau shi matsakaici ne. 

Annabi Muhammad (S.A.W) fari ne mai surkawa da jaja-jaja. Watau ba fari gau ba. Allah ya halicce shi da fuska mai haske. Yadda fuskarsa take a tsakanin mutane, kai ka ce farin wata ne, irin yadda yake haskaka sauran halittu na duniya. Yana da yalwar goshi da karan hanci. 

Yana da gashin ido da na gira, masu duhu. Yana da tsagar baki mai ɗan tsayi, ba tsukakkiya ba. Haka nan yankan tsagar idanunsa su ma suna da ɗan tsayi. Ƙwayar idanunsa fara ce tas, baƙin kuma baƙi suɗuk. Wuyansa yana da ɗan tsayi. Yana da wushirya a tsakanin haƙoransa na gaba. Gashin kan Annabi Muhammad (S.A.W) baƙi ne wuluk, kuma mai tsayi. 

Domin Karanta Bayani akan Yin Jadawalin Ayyukakn Rana Da Yini A Rubuce Danna Nan

Wani lokacin, Idan ya bar shi, ya kan kai iya kunnuwansa, daga bayansa. Kuma ya kan zuba a kan kafaɗunsa. Yana da gemanya mai duhu. Kuma yana barin ta ta yi tsayi. A ƙarshen rayuwarsa ya yi furfura a kansa da gemanyarsa, wadda ba ta fi ƙidayawa ba. 

Annabi Muhammad (S.A.W) yana da faɗin ƙirji. Wato akwai faɗi a tsakanin kafaɗunsa. Cikinsa ba shi da tudu. Yana da gaɓoɓi watau ƙasusuwansa suna da girma. Akwai gashi daga tsakiyar ƙirjinsa zuwa cibiyarsa. Akwai hatimin annabta a gefan kafaɗarsa ta hagu, daga baya.

Yana da tsayin hannaye madaidaita. Tafukan hannayensa suna da ɗan tudu da taushi. Ba a ƙarmashe suka ba. Haka nan kasangalalinsa da tafukan ƙafafuwansa. Amma ba shi da nama a agararsa. Wato agararsa a motse take. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi. 

Daga Is’haƙa ya ce:, “Na ji Barra’u yana cewa: “Manzon Allah (S.A.W) ya kasance ya fi kowa kyan halitta. Ba kuma gajere ba”. (Muslim ne ya rawaito). 

Daga Aliyu bin Abi Ɗalibin (RA), ya ce: “Annabi Muhammad (S.A.W) fari ne, mai cizawa da jaja-jaja” . (Albani ne ya ruwaito a cikin Aljami’us Sahihu). 

Daga Abdur Rahman ɗan Abdullahi ɗan Ka’abu ya ce. “Abdullahi ɗan Ka’abu ya ce: “Na ji ka’abu ɗan Maliku yana bayani game da (abin da ya faru sanda Allah ya karɓi tubansu na rashin zuwa masallaci), ya ce: “Na yi sallama ga Manzon Allah (S.A.W) alhali fuskarsa tana ƙyalƙyali saboda farin ciki ya kasance idan ya yi farin ciki sai fuskarsa ta yi haske, kai ka ce wani yanki ne na farin wata. Mun kasance muna gane haka game da shi”. (Bukhari ne ya ruwaito). 

Galibi ana siffata fuskar Annabi Muhammad (S.A.W) da farin wata, saboda haske da walwala da fuskarsa ta kan yi (musamman) a yayin da yake cikin farin ciki. Wannan yana nufin cewa, kamar yadda farin wata yake a duniya, to haka Annabi yake a cikin mutane. 

Amma a wannan Hadisin na Ka’abu bin Malik ya ware wani kashi ne na wata, domin yin ishara da goshin Annabi Muhammad (S.A.W), inda hasken ya fi bayyana, a sanda yake cikin farin ciki. Shi ya sa ya keɓance shi da wani yanki na wata4

Daga Abu Is’hak ya ce: “An tambayi Barra’u (R.A), shin fuskar Annabi Muhammad (S.A.W) kamar (hasken) takobi take? Sai ya ce: “A’a”, kamar (hasken) wata take” (Bukhari ne ya ruwaito).

Daga Jabir ɗan Samratu, ya ce: “Manzon Allah (S.A.W) ya kasance mai faɗin baki, mai tsayin yankan idanu, Mai siraren maƙyangyama…” (Muslim ne ya ruwaito). 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna Nan

labarin da ya wuceƘa’idoji Goma Sha Ɗaya Na Samun Nasara A Rayuwa
Labarin na GabaƊabi’un Annabi Muhammad (S.A.W) Dahalayensa