Halayen Annabi Muhammad (S.A.W)

0
29

Bayan Allah ya halicci wannan Annabi Muhammad (S.A.W) nasa da kyan halitta da kyan ɗabi’a sai kuma ya ɗora shi bisa kyawawan halaye. Shi da kansa (SWT) ya yabe shi da cewa: 

A nan za mu ga cewa duka wani kyakkyawan hali, Annabi Muhammad (S.A.W) ya suffatu da shi. Ga kaɗan daga cikin misalansu: 

GASKIYARSA (S.A.W): Gaskiyar ita ce, abin da mutum ya faɗa, ya zama haka ya ke a zuciyarsa, ya kuma dace da abin da yake a sarari. Haka kuma mu’amalar da mutum ya yi a bayyane ta zama haka take a zuciyarsa, matuƙar ba da wani dalili na shari’ah ba. 

Abin nufi a nan shi ne, Manzon Allah (S.A.W) ya kasance mai gaskiya tun a ƙuruciyarsa. Wannan ya sanya a sanda zai isar wa Ƙuraishu da aiken Allah sai da ya tara su ya ce da su: “Shin kuna ganin idan da zan ba ku labari cewa: “Ga dawakai nan a cikin kwari, suna nufin kawo muku hari, za ku gasgata ni?. Sai suka ce: “Na’am. Ai ba mu taɓa samun ka da wani abu ba sai gaskiya”. (Bukhari ne ya ruwaito). 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

Wani zai ce, to mene ne ƙarashen ƙissar? Ai a sannan cewa ya yi dasu: “Ni Manzo ne gare ku daga Allah, wanda idan ba ku yi imani ba azaba mai raɗaɗi za ta biyo baya”. Sai suka yi shiru, kamar za su gasgata shi. Amma ina! Baffansa Abu lahab shi ya yi wata mummunar Magana a gare shi, sannan y ace: “Yanzu domin wannan ka tara mu?. Dagan nan ya ɓata lamarin. 

AMANARSA: Mu sani cewa, amana ba ta taƙaita ga ajjiyar dukiya kaɗai ba. Watau a bai wa mutum ajiyar dukiya ya kawo ta yadda ta ke. Amana ta haɗa da amanar aiki (ka aiwatar da shi babu ha’inci) Amanar aiki (ka isar da shi daidai) Amanar aike (ke isar dashi da-idai). Amanar Magana (ka riƙe ta kada ka gaya wa wani). Ga kuma amanar gaɓɓai (kada ka aikata abin da Allah ya haramta dasu). Da sauran amanoni makamantan waɗan nan. 

Manzon Allah (S.A.W) ya kasance ya shahara da amana tun kafin ya zama Manzo. Misali, tun kafin aiko shi suna yi masa laƙabi da al’aminu. Nana Khadija ta nemi ya yi mata fatauci da dukiyarta saboda labarin amanarsa da ta ji. Mutanen Makka suna ba shi ajiyar dukiyarsu saboda amanarsa.

Harma lokacin da zai yi hijira ya dakatar da sayyidina Ali, domin ya basu amanoninsu. Kai a taƙaice dai a Tarihi cike ya ke ba bayanin wahalar daya sha (S.A.W), wajen isar da amanar aiken da Allah ya aiko shi da shi. ` 

CIKA ALƘAWARINSA: Annabi Muhammad (S.A.W) YA KASANCE MAI CIKA ALƘAWARI. Akwai misalai masu yawa ga me da haka. Ɗaya daga cikinsu shi ne, abin day a faru a sanda ake ƙulla sulhun Hudaibiyya. 

Ɗaya daga cikin yarjjejeniyar da aka rubuta akwai cewa, idan wani daga cikin kafiran Makka ya gudu Madina, a dawo da shi.. Amma idan ɗaya daga cikin musulmi masu hijira ya dawo Makka a ƙyale shi. 

To bayan an rubuta wannan, kafin a sa hannu, sai ga wani mutum da ake kira Abu jandal ya gudo daga hannun kafirai. Ya faɗo cikin Musulmi. Sai suhaili, (wanda ya ke wakiltar Ƙurashu ya ce: “Wannan shi ne wanda za a fara mayarwa”. Sai Annabi Muhammad (S.A.W) y ace: “Ai ba a gama rubutun sulhun ba”. 

Sai mutumin nan Ya ce: “To in haka ne ba zan yi sulhun da kai ba”. Annabi Muhammad (S.A.W) ya yi, ya yi, mutumin nan ya ƙi yarda. Abu jandal ya dinga kuka yana cewa: “Yanzu mayar da ni za ku yi cikin kafirai, su fitini addinina! Sai Annabi Muhammad (S.A.W) ya ce masa: “Yi haƙuri Abu jandal. 

Domin Karanta Bayani akan Yin Jadawalin Ayyukakn Rana Da Yini A Rubuce Danna Nan

Mun riga mun yi alƙawari da waɗan nan mutanen. Ba za mu saba ba. Allah zai ba ka mafita, kai da sauran raunana da ke tare dakai”7. Wannan babban misali ne na cika alƙawari, wanda ba a taɓa samun irinsa ba. Ba ma haka ba, saboda muhimmancin cika alƙawari Manzon allah (S.A.W) ya nuna baya tare da mai saɓa alƙawari, kuma ba shi, ba shi ranar alƙiyama. 

7 Bukhari ne ya ruwaitoDaga Amru binil Hamƙi y ace: “Na ji Annabi Muhammad (S.A.W) yana cewa: “Wanda duk wani ya ba shi amincin ransa, sai kuma ya kashe shi, to ba-ni ba-shi, wanda ya yi kisan. Ko da kuwa wanda aka kasha ɗin kafiri ne” (Barrazu ne ya ruwaito a musnad ɗinsa).

KARAMCINSA (S.A.W): Annabi Muhammad (S.A.W) ya zo da wani sabon launi na karamci a tarihi, wanda ba a taɓa gani ba. Abin duniya bai taɓa rufe masa ido ba, in dai ta hanyar Allah zai bayar da shi. Annabi Muhammad (S.A.W) mutum ne wanda ba ya tsoron talauci. Ga wani misali kaɗan na kkyautarsa a yaƙin Hunainu: 

A shekara ta takwas da Hijra bayan Annabi Muhammad (S.A.W) ya bude Makka, sai ya taho da mutum ɗari biyu sababbin musulunta, zuwa yaƙin Hunainu. Don haka rundunar Annabi Muhammad (S.A.W) ta zama mutum dubu goma sha biyu. 

Yayin da aka kamala yaƙi, sai ya zama an sami ganima mai yawa. A nan ne fa Annabi Muhammad (S.A.W) ya yi kyauta ta fitar hankali ga sababbin musulunta, domin ya ja hankalinsu su tabbata a wannan addini. 

Annabi Muhammad (S.A.W) ya bai wa Abu sufyanu (shugaban Makka a wannan lokacin) ruƙumi ɗari, da uƙiya arba’in na dirhami. (watau dirhami dubu da ɗari shida). Sai Abu sufyanu ya ce: “To ga ɗana yazidu”. 

Sai Annabi Muhammad (S.A.W) ya ba shi kwatakwacin haka. Sai ya sa ke cewa: “Ga kuma ɗana Mu’awiya”. Sai shi ma ya ba shi kwatankwacin haka.a nan ya baiwa hakimu bin hizam raƙumi ɗari. Ya nemi ƙarin dinare dubu, ya ƙara masa. Ya bai wa safwanu bin Umayyata dinare dubu. Ya qara masa wata dubun. Ya kuma qara masa wata dubun8

TAUSAYINSA DA NUNA ƘAUNA GA YARA: Annnabi Muhammad (S.A.W) yana da matuƙar nuna tausayi da ƙauna ga ƙananan yara. An ruwaito Hadisai kamar haka: 

Daga Nana A’isha (RA) ta ce: “Wasu mutane sun zo wa Annabi daga larabawan ƙauye, sai suka ce: “Ku kuna Sumbatar ƴaƴanku?. Sai aka ce musu “Na’am”. Sai suka ce: “Mu kuwa wallahi ba ma sumbatar su”. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Ban tabbatar ba ko Allah ya cire muku tausayi. Watau daga zukatanku”. (Muslim ne ya ruwaito). 

Duba Ar Rahiƙul Makhtum al Mubarakafuri, Shafi na: 361. Ya curo daga littafin As daga littafin As Shufa na Alƙali Iyad.

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna Nan

Daga ‘Usamatu bin Zaid (RA), ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya kasance ya kan ɗauke ni ya ɗora ni a kan cinyarsa. Ya ɗora Hasan a kan ɗaya cinyar: Sannan ya rungume mu. 

Sannan ya ce: “Ya Allah! Ka ji tausayin su. Ni ina jin tausayin su (Bukhari ne ya ruwaito). 

Daga Abdullahi bin Abbas (RA) ya ce: “Lokacin da Annabi Muhammad (S.A.W) ya isa Makka (a shekarar da aka buɗe Makka), sai `ƴan ƙananan yara na Banu Abdul Muɗɗalib suka tare shi. Sai ya rungume ɗaya a ƙirjinsa. YA goya ɗaya a bayansa” (Bukhari ne ya ruwaito). 

HAƘURINSA GA MASU YI MASA WAUTA: Annabi Muhammad (S.A.W) ya kasance mai haƙuri da kau da kai ga wanda ya nuna masa wauta ko rashin hankali. Ga wasu misalai ga me da haka: 

Daga Anas bin Malik (RA) ya ce: “Na kasance ina tafiya tare da Annabi Muhammad (S.A.W) yana sanye da mayafin Najaranu mai kaurin geza, sai wani Balaraben ƙauye ya riske shi, ya fisgi mayafinsa da ƙarfi, har sai da na ga alamar fisgarsa da ya yi a kafaɗarsa, Sai ya ce: “Ya Muhammad! Yi umarni a ba ni daga dukiyar Allah wadda ta ke wajenka. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya waiwaya gare shi, ya yi murmushi. Sannan yayi umarni a yi masa kyauta” (Bukhari da muslim su ka ruwaito). 

Daga Ubaidullahi bin Abdullahi bin Utbatu (Ya ce,) Abu Huraira ya ba shi labari cewa, wani Balaraben ƙauye ya yi bawali a cikin masallaci (masallacin Annabi Muhammad (S.A.W)). Sai mutane suka yi kansa, za su doke shi. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Ku ƙyale shi. Ku zuba rabin guga (ko cewa ya yi ) cikin guga na ruwa. An aiko ku masu sauƙaƙawa. Ba a aiko ku masu zafafawa ba” (Bukhari ne ya ruwaito). 

ZUHUDUNSA (WATAU RASHIN DAMUWA DA DUNIYA): Yadda Annabi Muhammad (S.A.W) ya gudanar da rayuwarsa ya nuna ko kaɗan bai damu da jin daɗin duniya ba. Ya kasance yana kwanciya a kan tabarma tsirararta, da matashi wanda aka cusa masa zarbar dabino. Galibin abincinsa dabino da sha’ir. 

A kwai lokutan da akan shafe wata biyu ba a yi girki ba a gidansa, sai dabino da ruwa. Wasu maƙotansa ne masu kiwo su kan aiko musu da nonon awaki. Ga dai wasu Hadisai da su ke nuna irin rayuwar da ya yi (S.A.W).

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna Nan

Daga Nana A’isha ta ce: “Iyalin Annabi Muhammad ba su taɓa ƙoshi da abincin alkama ba dare uku a jere, tun daga sanda ya isa Madina” (Bukhari da muslim ne suka ruwaito). 

Daga Nana A’isha Manzon Allah (S.A.W) ya rasu, alhali bai taɓa ƙoshi da gurasa da mai ba sau biyu, a rana ɗaya” (Muslim ne ya ruwaito). 

Daga Anas bin Malik (RA), ya ce: “Annabin Allah (S.A.W) bai taɓa cin abinci a kan tebur ba ko a cikin faranti ko gurasa da romo”.10 

Daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Manzon Allah (S.A.W) ya ce: IDan da a ce, ina da zinare kwatankwacin dutsen uhudu, ba zan ji daɗi ba a ce na yi kwana uku da ragowarsa a tare da ni. Sai a bin da zan ajiye domin na biya bashi” (Bukhari ne ya ruwaito). 

JARUMTAKARSA (S.A.W): Annabi Muhammad (S.A.W) jarimi ne, wanda ba’a taɓa ganin irinsa ba. Ga dai abinda wasu daga cikin sahabbansa suke cewa: 

Barra’u bin Azib (RA) ya ce: “Wallahi duk sanda ya ƙi ya runcaɓe, da shi muke yin kariya. Jarumi daga cikinmmu shi ne wanda ya ke jeruwa da shi (Muslim ne ya ruwaito). 

Daga Anas (RA) ya ce: Annabi Muhammad (S.A.W) ya kasance ya fi kowa kyau. Ya fi kowa kyauta. Ya fi kowa jarumta. Wata rana mutanen Madina sun ji wata ƙara cikin dare. Sai mutane suka nufi wajen ƙarar. Sai Annabi ya tare su, alhali ya riga su zuwa wajen ƙarar, yana cewa: “Kada ku damu, kada ku damu”. Yana kan wani doki na Abu Ɗalha ko sirdi babu. Yana rataye da takobi…” (Bukhari da muslim suka ruwaito). 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna Nan

labarin da ya wuceƊabi’un Annabi Muhammad (S.A.W) Dahalayensa
Labarin na GabaKoyi Da Annabi Muhammad (S.A.W)