Sauro Halittar Allah Mai Ban Alajabi

0
242

Yayinda dan Adam yakeda idanu guda 2 domin gani, shin ko kasan da cewar sauro yanada idanu samada guda 100 masu suna mini eyes kuma kowanne guda 1 a cikinsa shima akwai samada guda 100 da ake kirada lenses, kuma kowanne da irin aikinsa ?

Dalilin hakanne yasa bazaka iya kasheshi farat daya ba ko da kuwan ka biyo ta bayansa. Irin wannan dalilinne yasa aka kwaikwayi idon sauron ta hanyar qirqiro CCTV camera, drones, motoci masu tuqa kansu da kansu da ake kirada self driving cars, dadai sauransu. Allahu Akbar !

Shin ko kunsan da cewar macen sauro ce take cijo bawai namijin ba ?

Shi aikin namijin shine: ya sadaukar da rayuwarsa ta hanyar jan hankalin mutum domin macen (wato matarsa) ta samu damar zuqar jinin da zata samarda isassun qwayayen da zata qyanqyashe ta yanda za’a kara samun wasu yayan sauron, kenan hakan yana nufin ta cikin jininmu suke samun qwayayensu, wanda a qalla macen sauro tana qyanqyashe qwayaye guda 100 zuwa 200 a lokaci daya, Allahu Akbar !

Allah mai yanda yaso !

Yayinda ya zamana Allah SWT ya haliccemu da zuciya guda 1, shin ko kunsan da cewar sauro yanada zuciya har guda 3 ?

Akwai left ventricle akwai right ventricle sannan kuma akwai central ventricle kuma cikin ikon Allah, kowacce da irin aikin da takeyi a jikin sauron

Sauro itace halittar da tafi kowacce halitta yawan kashe dan Adam ta hanyar saka masa cutar Malaria, Zika dakuma West Nile. A qalla da akwai ire-iren sauraye a duniya sama da 3,500 wadanda suke satar jinin dabbobi kama daga mijizai, kifaye dakuma mutane domin su samarda qwayayensu

Sauro na iya ganin mutum a cikin mosquito net batareda wani shamaki na bango ba, a maimakon mu da muke amfanida haske domin gani, shikuma sauro yana amfanida iskar Carbon dioxide ne wadda yakan iya shakar numfashinka daga nisan qafa 150, hakan ke basu damar gano blood group dinka, wanda indai baiyi daidai da nasu ba, bazasu sha jininba, Allahu Akbar !

To ya akai mukasan wannan ilimin ?

Allah cikin ikonSa ya bawa Professor Jeffery Riffel (Malamin Biology a Jami’ar Washington ta Amurka) ikon gano dabi’un sauro dakuma yanda sauron yake tunani. Lokacinda ya bude qoqon kan sauron wanda ake kirada cuticle yaga qwaqwalwar sauron, kamar yanda ya zanatawa manema labarai. Sun gano hakanne bayan shafe shekaru samada 12 shi da abokan aikinsa (team)

Shin ko kunsan sauro yana kada fika-fikansa sau 1000 a cikin second 1?

Yayinda macen sauro take sokawa fatar mutum allurai 6 da suke a bakinta, a lokacinne namijin sauro yake jan hankalin mutum don aikin macen ya kammala ba tareda mutum ya farga ba. Dukda cewar ma kafin kaji zafin cizon sai an dauki yan sakwanni saboda allurar sedative da take tsirawa fata domin kashe zafin cizon, yayinda aikin ya kammala ita kuma ta riga ta bar fatar a lokacinne zafin cizon zai fara tasiri akan fatar mutum, yayinda kakai duka kuma tuni ta dade da tsotsar adadin jinin da take buqata. Allahu Akbar !

Wannan duk ba abin mamaki bane domin kuwa idan muka koma cikin littafin Allah SWT, Al-Qur’ani mai girma to zamu tabbatarda cewar ikon Allah ya wuce duk yanda yar qaramar qwaqwalwarmu take tunani. Allah SWT yace a cikin Suratul Baqara ayata 26 “Innallaha layastahyi anydriba, masalamma ba’udatan fama fauqaha” ma’ana “Lalle ne, Allah ba ya jin kunyar ya buga misali kowanne irine, SAURO, da binda yake bisa gareshi”. To anan tunda kaji misalin sauro ya fito a cikin Qurani kaikasan yanada abubuwan al’ajabi kam

Wannan kadan daga cikin bayanine akan halittar sauro, daya daga cikin ziliyoyin halittun Allah SWT, duk Allah ya bawa masu ilimin kimiyya wannan damarne domin su gane ayoyinsa da suke sararin sama’uddunya dakuma kan duniyarmu ta Ard damuke rayuwa

Muna roqon Allah ya qara mana imani dakuma jin tsoronsa, ya tabbatardamu akan bin sunnar ma’aiki ya rabamu da bidi’a ya nesantamu daga azabar wuta sannan kuma ya sakamu a AljannarSa don RahamarSa ba don halinmu ba

Tura saqon zuwaga sauran yan uwa domin mu amfana da ilimin baki daya

Ga wadanda basuga amsar tambayoyinsu ba, zan turo amsoshinku a kashi na 2, insha Allahu

✍Usman Danliti Mato, A Public Writer, A Media Aide to Several Personnel (A Co-founder Usmannoor Media BUK)

WhatsApp contact: 07035387476 Facebook: Usman D. Mato

labarin da ya wuceSujjada kabli
Labarin na GabaTarihin Kano