Tarihin Kano

0
173

Idan ana so a nakalci Tarihin Kano sosai, dole ne sai an tabo tarihin kasar Hausa. Shi kuma tarihin kasar Hausa sai an leka cikin tarihin Sudan. Shi kuma tarihin kasar Sudan sai an lelleka cikin tarihin daular Larabawa ta Banu Ummayyata da ta Banu Abbasi. Har ila yau kuma da binciken labarin wani tunzuri da ya sa jama’a suka rika kauratowa daga tsakiyar kasar Asiya suka yi wo yamma.

Kasar Sudan itace yankin kasar Afrika na wajen tsakiya, daga gabas ta iyaka da kasar Habasha (watau Ethiopia), daga arewa ta yi iyaka da Sahara daga kudu ta yi iya da yankin gabar Tekun Atlantic da ake kira ‘Gulf of Guniea’ — da kuma kasashen sunkurun kurmin nan na tsakiyar Afrika. Kalmar nan ‘Sudan’ ma’anarta baki, saboda galibin al’ummar da ke zaune a cikin yankin Sudan masu bakar fata ne. An ce zafin rana shi ke sa su baki (kunne ya girmi kaka), gama dukkan kasar Sudan tana daf da wurin da ake kira ‘Haddul Etidali’ watau ‘Equator’. Kasar Hausa ita ce yankin nan na kasar Sudan wanda ke wajen tsakiya-tsakiya. Daga gabas da ita ga kasar Borno; daga Yamma ga kasar Dahomey (wacce yanzu ake kira Jamhuriyar Benin); daga arewa ga Hamadar Sahara; daga kudu kuma ga kasashen Nupe da kasahen da ake kira ‘Middle Belt’. Kasar Kano tana daga yankin tsakiya na arewacin kasar Hausa. Daga gabas ta iyaka da kasashen Borno da Bauchi; daga yamma ta yi iyaka da Katsina; daga kudu ta yi iyaka da Zariya; daga arewa kuma tayi iyaka da kasar Neja. Tun daga yanzu za a fara fahimtar lalle Kano wajibi ne ta zama babbar alkarya saboda ita ce kamar tsakiyar kasar Sudan duka.


Taswirar birnin Kano

Tun da dadewa kasar Hausa da kuma sauran kasashen Sudan sun sami adabunsu na zaman duniya daga fuska biyu mabambanta —- watau Gabas da Yamma. Sa’adda sabawa ta sa jama’ar kasar Mangoliya ta Asiya suka rika fuskantowa yamma-yamma, a hankali sai masarauta ta rika kafuwa, in wannan ta fadi, wata kuma ta tashi a can gabas. Shi ne daga bisani mulkin Farisa, (watau persia), ya kafu, ya mallake kasashen gaba duka.

Mazaunan Farko

A kasashen Karni na Tara (9th Century) na Masihiyya wadansu maharba, wadanda babu hakikar daga inda suka zo suka zauna kan duwatsun da ke kewaye da sararin da ake kira Kano yanzu. Irin duwatsun nan sune irinsu Dala. Gwauran Dutse, Magwan da Dutsen Fanisau.
Su maharban nan suka rika yin farauta a wani kurmi wanda ya ke shine tushen rafin Jakara, inda kasuwar Kurmi ta Kano ta samo suna. dan wadannan maharba suka jarraba dan koma suka ga wurin yana da albarka, sai suka ci gaba suna kara saran dajin suna yin gonaki. Albarkar wurin nan mai ban mamaki sai ta jawo wadansu mutane daga wadansu wurare suna zuwa. Da taron mutanen wannan lokaci mai nisa, ya kan zama mutum ne da ke da fifikon karni game da tsafi.

Babu tahakikanin akan irin tsarin mulkin da wadannan al’umma su ka gina shugabacinsu, amma duk da haka ana iya cewa aikin shugaba a wannan lokaci bai wuce tsare dokokin farauta da kuma kusaci da tsafin da mutanen ke bautawa

An bayar da bayanan nan a karkashin littafin ‘Kano Ta Dabo Cigari’ wallafar Alhaji Abubakar Wazirin Kano.
ISBN: 978-140-501-2218

labarin da ya wuceSauro Halittar Allah Mai Ban Alajabi
Labarin na GabaYaren Soyayya A Mahangar Addini da Nazarin Kimiyyar Halayyar Dan Adam