Tarihin Dutsen Dala Da Rayuwa A Kewayensa

0
399

Dala

An fara ambatar Kano da sunan Jihar Kano daga lokacin da sojoji suka karɓi mulkin ƙasar nan, kuma suka yayyanka ƙasar zuwa jihohi, kafin wannan lokaci, cewa ake da ita lardin Kano, ko kuma a ce Kano da maƙwabtanta.

Shi wannan birnin na Kano, ya kafu ne tun lokacin da ba a sani ba, wanda hakan yasa aka samu mabambantan ra’ayoyi dangane da lokacin da Kano ta kafu, wasu suna cewa, “Kano ta kafu ne tun lokacin da ba a sani ba”. Yayin da wasu suke cewa, “Ta kafu ne tun lokacin jahiliya, kafin zuwan Musulunci”. Wasu ɓangaren suna cewa, “Ta kafu ne tun shekara ta 208 A.H (bayan Hijira), wasu sun ce a shekara ta 303 A.H. ko shekara ta 444 A.H. ko kuwa 906 A.D.

Kamar yadda aka yi saɓani a kan mazaunan ta na farko, inda wasu suka ce mutanen Gaya ne, waɗanda suke zuwa daga alkaryar Gaya, don ɗibar tama; a yayin da damuna ta sauka, sai suka zauna daga yammacin Dala; da wasu manyan rahoniyoyinsu masu kama da tsawon mutum, suna dafa tama a ciki bayan sun yi tsafe-tsafensu, idan ta haɗu, sai su yi ƙarfe da ita, ƙarfen shi ne suke ƙera kayen noma da yaƙi da kuma farauta, sai su bayar a musanya musu, a ba su abinci da sauran kayan buƙatu, waɗannan makera har yanzu akwai zuriyarsu suna yin ƙira.

Kuma, wasu ko sun ce ‘yan farauta ne, waɗanda suka haɗu da mutunen da suka tarar, suka yi ‘yar alkarya ƙarama, waɗannan su ne iyalan ƙasaitaccen mutumin nan da ake kira da ‘Dala’, wanda Dutsen Dala ya samo sunansa daga gare shi, don ya zauna a kan saman ‘Dala’ shi da iyalansa.

Bayan da Kanoki ya dawo Dala ya zauna, sai kasuwa ta buɗe masa. Mutane daga ko’ina suka riƙa zuwa wajensa, suna sayen kayan noma da na farauta da na aikin gidaje.

Wannan kasuwa sai ta jawo masa ƙabilu iri daban-daban, waɗanda suka yiwo ƙaura, suka zo wajensa don su zauna tare da shi. To da yake kowace ƙabila takan zo da abin da Allah ya hore mata na sana’a, sai  masana’antu suka tashi a gurin. Masakar tufafi da marina da majema duk suka yawaita.

Wannan ƙaramin buɗi na arzikin ƙasa, shi ne ya kawo kafa birnin Kano a gindin Dala, wanda ya ƙunshi dangin ƙabilu sha ɗaya. Kuma kowace ƙabila tana da sana’ar da ta kware a kai. Saboda sunan wannan makeri Kanoki da ya farazama a gurin ake kiran gurin Kano, kuma ƙabilarsa aka dinga kiranta Abagayawa.

Wannan ƙaramin juyi, ana zaton ya faru ne a tsakanin ƙarni na 5-6 daga haihuwar Annabi Isa (A.S) kuma su waɗannan ƙabilu guda goma sha ɗaya da suka kafa wannan birni a gindin Dala, za ka karanta su a nan gaba kaɗan, kamar yadda tarihin Kano ya ambace su.

Wani abin sha’awa cikin rayuwar waɗannan ƙabilu   shi   ne,  zaman   lafiya   da   haɗin kai na taimakon   juna.   Tun da dabarar yin sarki, a matsayin shugaban kowa da kowa, ba ta zo ba, to limamin addininsu shi ne shugabansu. A lokacin ruwan Jakara suke bautawa kuma Mazauda shi ne limanin bautar  Jakara,  saboda haka, ya zama shugaba.

To cikin waɗannan mutane ne, Dala ya zo ya zauna tare da su a kan dutsen Dala. An ce Dala ya zo wannan wuri tare da ‘ya’yansa guda bakwai, huɗu maza uku mata. Sunan babban su Gargaji, shi ne kakan Buzami uban   Barbushe, kuma Barbushe shi ne ya gaje shi daga baya.

Daga Ina Dala Ya Zo?

Malaman tarihin Kano irin su Alkali Zangi Waziri Abubakar ba su yi nishaɗi mai yawa ba, tare da labarin Dala da iyalinsa, balle a san daga ina ya zo, kuma shi wane ne kafin ya zo ɗin. Idan ban da  littafin  Tarihin  Kano  na  Muhammadu Bello (Sarkin Kano  1883-1892) ba wanda ya faɗi labarin Dala. Ko shi ma wannan littafin, bai faɗi wani abu mai tsawo ba a kan zuwan Dala nan ƙasar . Abin da littafin kawai ya faɗa shi ne:

“Shi Dala mutum ne baƙi kuma ƙaƙƙarfa, kuma mafarauci kwarai. Domin shi yakan kashe giwa da sandarsa, ya dauko ta a kansa, ya yi tafiya da ita kamar mil tara. Ya zo garin nan ba a san asalinsa ba. Da ya zo ya gina gidansa a Dutsen Dala, ya zauna a kanta shi kaɗai tare da matansa da ‘ya’yansa bakwai, huɗu maza, uku mata. Sunan babbansu Gargaji, shi ne kakan Buzami uban Barbushe. Barbushe ne ya gaji halayen Dala daga sanin dukkan dangogin tsafi da al’ajubansa da sihirinsa da rinjaye ga ‘yan uwansa, domin haka, ya zama shugabansu!”

To wannan abin da aka kawo maka cikin littafin Tarihin Kano game da Dala, shi ne kawai abin da za ka ji game da shi, ba daɗi ba ragi, Wannan kuwa ɗan bayani na Dala, ba zai ƙosar da duk wani almajirin Tarihin Kano ba. Kuma tun da yake babu   littattafai a ƙasar  Hausa a  yanzu, waɗanda za su taimake mu, su ba mu haske don mu san daga ina Dala ya fito, kuma da inda ya koyi sihirinsa da dabarar sarrafa su, don neman mu san daga inda ya fito.

To dole ne mu yi namu ƙoƙarin, Idan ka yi tsokaci mai nisa cikin abin nan da littafin Tarihin Kano ya faɗa game da Dala, za ka ga shi wannan mutum, ya zo da abubuwa uku waɗanda ba a san su a nan ƙasar ba, kafin zuwansa, kuma su waɗannan abubuwa da ya zo da su, su suka sa ya sami shugabancin matsafan wannan guri, har ya bar wa jikansa Barbushe wannan shugabanci.

Su waɗannan sababbin abubuwan dai da Dala ya kawo su ne:

  1. Dabarun gina wa gunki ɗaki na musamman, da sa masa ranar bauta, da sallar idi biyu; ƙaramar salla da babbar salla, kamar yadda ake bauta a Ka’aba a ƙasar Larabawa a zamanin jahiliyya.
  2. Dabarar sihirce-sihirce da tsafe-tsafe wanda ta burge mazauna wannan wuri, har suka yi wa Dala mubaya’a suka bi jikansa Barbushe da gunkinsa Tsumburbura bi na haƙiƙa.
  3. Dabarar sarrafa giwa wadda ta nuna cewa dama can kafin Dala ya zo nan kasar, ya san giwa da yadda ake sarrafa ta. Tun da yake waɗannan abubuwa da muka lissafa haka suke ga Dala, to shi Dalan daga ina ya fito? Kuma a ina ya sami sanin waɗannan dabaru nasa da aka ambata a sama?

Shehu Nasiru Kabara ya gaya min cewa, Dala ya zo ne daga tsibirin Dahlak na Rasar Habasha. Wannan tsibiri a bakin kogin Maliya yake, kuma a yanzu yana cikin Kasar Eritrea ne. To ka ga ashe Dala ya fito ne daga cikin ƙasashen gabas, waɗanda suka sami ci gaba wajen ilmin sihiri da tsafi da bautar gumaka da farauta irin ta wancan lokaci fiye da na mazaunan Kano na farko.

Don haka suka bi shi dole, ba don ra’ayi ba.

Amma a nazarin da Lugard  ya yi a kan tarihin Hausawa a cikin littafinsa mai suna Tropical Dependence ya ce, “Masu irin wannan addini na gunkin tsumburbura watakila Kibdawan Misira ne na ƙabilar Phonecian, wato Banu Kan’ana kamar yadda aka san su a ƙasar Hausa. Sabooda haka, Dala da jikansa Barbushe ana zaton kibɗawan Misira ne suka yiwo ƙaura daga tsibirin Dahlak na kogin Baharul Maliya, wanda a wannan lokacin a ƙarƙashin mulkin Fir’aun bin Inf yake. Da suka zo nan, suka mallake mutanen wannan   ƙasa na   farko;   ƙabilun  Kwararrafa saboda ci gabansu da ƙwarewarsu wajen tsafi da farautar giwa.

Zuwan Dala Da Aikin Hajji A Kano

Zuwan Dala wannan garin tare da iyalinsa da sauran jama’a da ya zo da su, ya kawo ci gaban mazauna wannan wuri na asali. Da farko dai, an samu auratayya tsakanin iyalinsa da mutanen wannan guri, wanda daga ƙarshe ta haɗe mutanen, har aka san su da ƙabilar Dala. Na biyu kuma Dala ya zo da sabuwar bautar gunki irin wadda ake yi a Makka ta su Lata da Uzza kafin Musulunci ya bayyana”.

Haka kuma, shi ne ya fara gina wa gunki ɗakin bauta mai kusurwa guda huɗu wanda ba mai shiga sai shi kaɗai, ya kirawo wannan gunki nasa Tsumburbura, (watakila wannan ya yi  kama da Kulaista Abraha Sarkin Yaman).

Bayan wannan, Dala ya sa wa wannan gunki nasa bikin idi a kowacce shekara wanda ake yi a daidai da lokacin da ake hawan Arfa da Babbar salla a Makka. Waɗannan sababbin  abubuwa  sun  bai  wa  Dala ƙarfin ɗaukaka   daga   mabiyansa   na   ko’ina   na ƙasar Kano. Wannan ɗaukaka ta Dala, ita ce ta haɓaka, har ta zama gadon gargajiya da ɗan jikansa, Barbushe ya gaji duk sihirinsa da tsafinsa, bayan shi ya mutu.

Game kuma da irin addinin da Dala ya zo da shi wanda ya sha bamban da bautar Jakara, ga abin da Malam Adamu naMa’aji ya fada a kai:

“Ana yin  bikin  Idi sau  ɗaya  a shekara, a (Dala), daidai da lokacin da ake yin Sallar Id-el- Adha a watan Zul Hajj a Makka. A ranar sallar Idi Barbushe, wanda shi ne babban Limami, shi yake jan duk mahajjata zuwa ɗakin gunkinsu, yana rike da baƙin bunsuru na layya. Idan an yanka wannan bunsuru, sai a zuba jininsa a cikin wata gidauniya, wadda aka ajiye a gaban gunkin.

To, a nan ne Barbushe zai saurari abin da gidauniyar za ta yi. Idan jinin ya yi sanyi a cikin gidauniyar to, alama ce ta komai zai daidaita a sami zaman lafiya da arziki a wannan shekara. Idan kuma jinin ya yi zafi to alama ce ta abin da zai faru a wannan shekara na dangin masifu. Yawan zafin jinin yawan abin da zai faru kenan ko, yaƙi ko annoba ko yunwa. Daga nan sai Barbushe ya shaida wa maƙarrabansa abin da ya gani na masifar da za ta afku, da kuma lokacin da za ta afku din.

Sannan kuma sai ya ba da umarnin kowane mahajjaci ya yi layya da abin da ya zo da shi don a roki gumaka su kare masifar da za ta zo, ko su rage ta, ta yi wa mutane sauƙi yadda za su iya jure ta”. Wani abin sha’awa a nan shi ne, irin wannan bauta da ake yi a Kano, ita Larabawa suke yi wa Lata da Uzza a Ka’aba a Makka, kafin bayyanar addinin Musulunci.

A cikin littafinsa mai suna Nuril Yakeen Fi Sirat Sayyadil-Mursalin, Sheikh Muhammad al-Hadhari ya bayyana irin gidauniyar da ake zuba jinin bautar gunki a Makka ta waccan lokacin, ya ce sunan gidauniyar “al-Nasab”, kuma dutse ne aka fafe shi ya zama gurin zuba jinin bauta. Koda yake a nan Malam Adamu na Ma’aji, bai faɗi sunan gidauniyar tsafi ta Barbushe ba, bai kuma faɗi siffarta ba, wataƙila gidauniyar tsafin Barbushe ta ƙarfe ce, wadda mutanen Kano suka ƙera masa, don irin wannan ibada ta gumaka.

Wannan siffar bautar gunkin Tsumburbura da Malam Adamu na Ma’aji ya bayyana, ta yi daidai da abin da littafin Tarihin Kano ya bayyana game da Idin da ake yi a Dala a wancan lokaci, kuma ga abin da littafin ya ce: Ya fara da nahiyoyin da ake tahowa Dala domin bikin Idi biyu; sallah karama da Sallah babba.“Tun daga Tudu zuwa Danbakoshi, daga Duji zuwa Dankwai, dukkansu suna taruwa wurin Barbushe daren sallah biyu, domin shi ne babbansu cikin tsafi.

Sunan wurin da gunkinsa yake “Kakuwa”, sunansa kuwa “Tsumburbura domin itaciya ce da ake ambaton ta “Shamus”, sunan mutumin da yake a zaune a karkashinta dare da rana “Mai Tsumburbura”. An kewaye itaciyar da gini, babu mai shiga cikin ginin sai Barbushe, dukkan wanda ya shiga sai ya mutu nan da nan.

Barbushe kuma ba ya saukowa daga dutsen Dala sai idan ranakun Idi biyu sun kusato. Sa’an nan mutane su zo masa daga gabas da yamma, kudu da arewa, maza da mata. Daga cikinsu wadansu su zo da bakin kare, wadansu da bakar kaza, wadansu da bakiin bunsuru“.

Wannan ita ce siffar gunkin Barbushe da masu bauta masa da kuma lokacin da suke yin wannan bauta, wato Salla babba da Salla ƙarama ko Kuma mu ce Hajji da Umra, kamar yadda ake yin su a Makka ta lokacin Jahiliyya.

Ban da wannan kuma ga yadda suke yin hawan arfa  da Ɗawafi i na jahiliyya, bayan su kuma su yi layya “Idan sun taru a ƙarƙashin dutsen Dala ranar jajibri (ranar Arfa) bayan la’asar, sa’an nan Barbushe ya fito daga gidansa da Isha tare da makaɗansa (na Kuru da Gunduwa da Tsintsima). Ya riƙa kururuwa da ƙarfi yana cewa; “Babban Jimina akasa mun gama karaga ga laya Tsumburbura”.

Mutane kuma su ce, ga Tsumbirbirar Kanawa, ga wajen Dala”. Bayan wannan ya sauko su tafi tare da shi zuwa wurin gunki. Da isa wurin gunkin, kowa ya yanka abin da ya zo da shi, sannan Barbushe ya shiga cikin ginin shi kaɗai yana cewa, Magajin Dala, da kun ƙi da kun so ku bi, ni ba ra’ayi ba‘. Su kuma su ce,

“Maigida bisa kan dutse, ubangijin Mama, bi mun bi ka, ba a ra ‘ayi ba”. Suna faɗar wannan suna kewaye ginin (suna dawafi) har hudowar alfijir, sa ‘an nan su tsaya tsirara su ci abinci.

Ya fito, ya ba su labarin dukkan abin da zai faru cikin dukkan wannan shekara, har da bakon da zai fuskanto zuwa wannan gari, ko na alheri ne ko na sharri ne. Shi ne ma ya ba su labarin gushewar mulkinsu da sarewar itaciyarsu da Konewarta da ginin wannan masallaci.

Kuma ya ce musu wani mutum zai zo wannan gari tare da rundunarsa, ya mallake mu”. Suka ce masa “don me ka fadi wannan? Wannan magana ce mummuna, ya yi shiru. Sa’an nan ya ce da sannu ku gan shi da alfarmar Tsumbirbura! Idan bai zo a zamaninku ba, ya zo a zamanin ‘ya’yanku, ya mallaki dukkan wanda ya samu a cikin wannan ƙasa dukkanta, ya sa a manta da ku duk da jama’arku, ya kuma bayyana da ƙabilar tasa zamani mai tsawo.”

Wannan duba na Barbushe bai yi wa mabiyansa daɗi ba, don haka suka yi bakin ciki kwarai suka ce masa, “Yaya za mu yi mu kawar da wannan al’amari? Ya ba su amsa da cewa ba yadda za ku yi, sai hakuri. Watakila Barbushe ya hango wani gagarumin juyi, wanda ƙabilar Madatai za ta zo da shi wanda zai haɗiye ƙabila tasa da sannu, shi ya sa ya yi wannan duba cikin tsafinsa, ya ga abin da ya gani na wannan juyi, ya gaya wa mabiyansa.

Kogin Jakara

Koda yake waɗannan ƙabilu ba lokaci ɗaya suka zo Kano ba, kuma ba gaba ɗaya suka zo ba, a’a kaɗan-kaɗan suka dinga zuwa, har suka taru suka yi ƙungiya iri biyu, kungiyar Dala ta masu bautar gunki, wato Tsumburbura da kungiyar ‘Yan farauta. Lokacin da wadannan kungiyoyi suke zaune a Kano suna zaune kusa da juna, amma kogin Jakara da manya-manyan itatuwan da suke kewaye da kogin su ne suka raba su, ƙabilar Dala tana arewa da ita, ƙabilar Madatai tana kudu da ita.

Ita dai Jakara wata ƙorama ce wadda ta faro daga wani guri, yammacin birni, wanda ake kira Bulbula, a Aisami, gabas da Gwauron Dutse. Ta keta ta Dausayi ta Karofin Wanka-da-Shuni, ta cikin Kasuwar kurmi, ta yi gabas har ta je Wasai ta garin Minjibir, ta miƙe da tafiya har ta kai Duku, ta ƙasar Garkin Dirani, inda ta ƙare , ba ta sake tafiya ko’ina ba.

Wannan ƙorama da duhuwarta, su ne suka raba waɗannan ƙabilu gudu biyu, kamar yadda muka faɗa a baya. To su waɗannan ƙabilu tun zuwan su, sun tarar da mazauna wannan guri na asali, suka zauna tare da su, suka koya musu irin sababbin dabarun zaman duniya da suka zo da su inda suka yiwo ƙaura, waɗanda mazauna wannan guri na asali ba su san su ba.

Kafin Dala, kakan Barbushe ubangijin Tsumburbura, ya zo wannan gari, akwai mutane da suke zaune a nan suna rayuwa irin tasu.

Mutanen da suke zaune a wannan guri, kafin zuwan Dala Kabilu ne iri daban-daban, kuma suna zaune ne zama irin na rinji. Zaman rinji shi ne zaman da kowane maigida yake zaune da ƙungiyarsa, a waje ɗaya, wadda ta haɗa gidansa da gidan ‘ya’yansa da na ƙannensa da kuma na barorinsa, ko kuma na waɗansu mutane daban da suka kawo caffa gurinsa don ya riƙe su, kamar ‘ya’yansa.

Kowane rinji akwai sana’ar da aka san shi da ita, kuma mutanen da suke zaune cikin rinjin an san iyakar wuraren da suka mallaka don noma da waɗansu ayyuka na sana’a.

Kamar yadda littafin Tarihin Kano ya fada, wasu daga cikin mutanen da Dala ya samu a nan, suna zaune ne kusa da kan Dutsen Dala, inda shi kansa ya hau ya gina nasa gidan. Waɗannan mutane kamar yadda Tarihin Kano ya bayyana, su ne: Gunzago mai gida a ƙarƙashin Goron-Dutse a Ga-giwa, wanda yake kama giwa da igiya don ƙarfinsa da Gubanasu da Ibrahim da Bardoje da Nisau da Kamfatsu da  Duje da Janberi da Gamakora da Gaftaro da Hangugu da Kar-dangi.

Waɗannan mutane su ne littafin Tarihin Kano ya bayyana su da cewa su ne muƙarraban Barbushe, jikan Dala. Wataƙila ma auratayya ce ta haɗa kakanninsu da ƙabilar Dala; wadda ya zo da ita, har wannan dangantaka ta shiga tsakaninsu.

Har ila yau; akwai wasu Rinjinan (Rijau) da shugabanninsu suka yi caffa ga Dala da gunkinsa; koda yake su ma zaman kansu suke yi, kuma nesa da Dala suke. Waɗannan kabilu su ne:
  1. Ƙabilar Danburu wanda yake zauna a Jigirya, wajen mil goma gabas da Dala.
  2. Ƙabilar Jandamisa wanda ake kira Ruma. Shi kuwa a kan Dutsen Magwam yake, wato Nassarawa ta yanzu; kuma ƙabilar wannan mutum wato Rumawa sun fi kowace ƙabila yawa a Kano a wancan lokacin. Domin su ne suka yaɗu tun daga inda suke, har zuwa Salanta wato kudu da Dala kamar mil goma.
  3. Ƙabilar Hambarau waɗanda suke zaune a kan Dutsen Tanagar.
  4. Ƙabilar Nisau wadanda suka zauna a kan Dutsen Fanisau. Shi Nisau shi ne uban Gumban ɗaya daga cikin manyan da suke bin Tsumburbura da Barbushe.

Domin karanta cikakken bayani akan Taƙaitaccen Tarihin Kano Kashi Na Ɗaya(1) danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Taƙaitaccen Tarihin Ƙasar Hausa danna nan.

labarin da ya wuceIdan Nayi Haɓo Da Azumi A Bakina, Yaya Azumina Zai Kasance?
Labarin na GabaMatsayin Koke-koke Da Kururuwa
Halliru A Abubakar
Sunana Halliru Adamu Abubakar. An haife ni a 19-1-1959. Ni mai fassara ne.