Taƙaitaccen Tarihin Kano Kashi Na Ɗaya(1)

0
891

Taƙaitaccen tarihin Kano kashi na ɗaya

Kano na ɗaya daga cikin manyan birane a ƙasar Hausa. Kano ita ce cibiyar kasuwanci ta Nijeriya gaba ɗaya, jihar Kano tana da ƙananan hukumomi guda arba’in da hudu(44).
Kano gari ne da yake da masarauta mai ɗumbin tarihi, Masarauta ce mai kwarjini a cikin Ƙasashen Hausa da kewaye.
Haka kuma, Kano gari ne babba wanda mazauna cikinsa suna magana da harshen Hausa. Kano shi ne gari mafi yawan jama’a a Nijeriya gaba ɗaya.
Cikin birnin Kano akwai ƙofofi kamar haka:Kofar Gadon Kaya, Kofar Famfo, Kofar Na’isa, Kofar Nassarawa, Sabuwar Kofa, Kofar Mazugal, Kofar Dawanau, Kofar Dan Agundi, Kofar Duka wuya, Kofar Ruwa, Kofar Kansakali da kuma Kofar Mata.
Kano gari mai tarin mutane da tasirin Sarauta
Yawan mutanen da suke garin Kano ya haura kimanin mutane miliyan goma (10,000,000) a ƙidayar da aka yi a shekara ta alif dubu biyu da shida (2006).
Kano tana da matukar tasiri a yawan mutane a Nijeriya, saboda ita ce ta fi kowace jiha yawan mutane a Najeriya.
Idan ka zo Kano, za ka samu mutane daga ko’ina a fadin duniya, tun daga na Kudancin Nijeriya, zuwa ƙasashen dake makwabtaka da Nijeriya, haka kuma, za ka tarar da mutanen Sin, wato (china), da kuma na kasashen Larabawa har da Turawan Yammacin duniya. Mutanen Kano sun shahara wajen addini sosai.
Sana’ar Rini
Al’ummar Kano sun kasance masu son sauraren rediyo
Kano ta yi suna wajen kasuwancin da ta bunƙasa a kai, har ya zamana ana cewa da ita Cibiyar Kasuwanci, haka kuma tarihin Kano ya nuna daman can Kano tana da suna wurin cinikayya tsakaninta da mutanen Gabas ta Tsakiya
Domin karanta takaitaccen bayani akan jihar kano danna nan
labarin da ya wuceTakaitaccen Bayani A Kan Jihar Kano.
Labarin na GabaYadda Ake Sharɓar Dankali
BHM Ninja
Sunana Buhari Ibrahim Aliyu [Googler] dalibin computer, digital marketer, technical crew a wikihausa dalibi mai kokarin yada ilimi na na'aura mai kwakwalwa tare da tabbatar cigaban kasuwancin zamani.