Yadda Ake Sharɓar Dankali

0
706

A yau za mu koyi yadda ake Sharɓar Dankali

Abubuwan Da Ake Buƙata

 • Kayan ciki
 • Dankalin Turawa
 • Kayan ƙamshi
 • Sinadarin ɗanɗano
 • Kayan miya
 • Ganyen fasali

Yadda Ake Haɗawa

 1. A samu kayan ciki na rago ko tunkiya, sai a wanke shi tas.
 2. A fitar da duk dauɗar da ke maƙalewa, sai a yanka su ƙanana, sannan a ɗora a wuta.
 3. Sai a zuba kayan kamshi da sinadarin ɗanɗano da gishiri a zuba albasa da tafarnuwa mai yawa.
 4. Sai ki bar shi ya dahu, Sannan a fere dankali a yanka shi ƙanana a kwance.
 5. Idan an tabbatar kayan cikin sun dahu, sai a ɗauko jajjagen kayan miya a zuba a ciki, tare da man girki.
 6. Idan ya yi kamar minti biyar, sai a zuba dankalin nan da aka yanka a ciki.
 7. Sai ki zuba sinadarin dandano a ciki ki juya, a bar shi ya dahu. Amma fa shi wannan girkin ruwa-ruwa ake cin sa.
 8. Don haka, idan ana dahuwar za a tafasa ruwa, a ajiye a gefe ko akwai buƙatar ƙarawa. Idan ya dahu sai a sauke, a ci shi da ruwa-ruwa.

Domin sanin Yadda Ake Plantain Pie danna nan

labarin da ya wuceTaƙaitaccen Tarihin Kano Kashi Na Ɗaya(1)
Labarin na GabaYadda Ake Shinkafa ‘Yar Senegal
BHM Ninja
Sunana Buhari Ibrahim Aliyu [Googler] dalibin computer, digital marketer, technical crew a wikihausa dalibi mai kokarin yada ilimi na na'aura mai kwakwalwa tare da tabbatar cigaban kasuwancin zamani.