Yadda Ake Haɗaɗɗiyar Miyar Gyaɗa

0
1879

Ko kun san miyar gyaɗa na ɗaya daga cikin miyar da ake yawan ci a Arewacin Nigeria. Miyar gyaɗa na da matuqar amfani ta inda zance a tattara sinadarai masu amfani kamar a cikin nama akwai protein, allayu akwai minerals, sannan ita kanta gyaɗa ta ƙunshi sinadarai masu yawa.

Miyar na iya zama abinci mai lafiya ga masu ciki da masu shayarwa.

Abubuwan Da Ake Buƙata

  1. Soyayyar gyaɗa (cup ɗaya)
  2. Tumatir (4 manya)
  3. Tattasai (2 manya)
  4. Attaruhu (yadda ake buqata)
  5. Albasa da allayyahu (babba)
  6. Nama ½ kg
  7. Sinadarin ɗanɗano (4)
  8. Curry, thyme, tafarnuwa, blackpepper
  9. Gyaɗar miya, daddawa ½ teaspoon \
  10. Manja da man gyaɗa (2 tablespoon)

Yadda Ake Haɗawa

  1. A wanke kayan miya da tafarnuwa a jajjaga
  2. A ɗora nama a sa albasa, curry, thyme da maggi a bar shi ya dahu, sai a tsame
  3. A cikin tukunya mai zurfi a soya manja da man gyaɗa sai a saka nama a ɗan ba shi tsaro na minti 3-4
  4. A zuba kayan miya, shi ma a soya shi da kyau sai a zuba da gyaɗa, kayan ƙamshi da sinadarin ɗanɗano
  5. A zuba romon nama idan ya ɗan juya, sai a ɗauko wankakken allayahu a zuba
  6. A bar shi na minti 2-3 sai a kashe wuta kar a bar allayahu ya dafe.

Domin sanni Yadda Ake Groundnut Sweet Potato Balls danna nan.

labarin da ya wuceYadda Ake Groundnut Sweet Potato Balls.
Labarin na GabaYadda Ake Haɗa Hallaka Kwabo