Yadda Ake Yin Ƙuli-ƙuli

0
1297

Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a saukake. Tare da ni Hafsat Shettimah. A yau za mu koyar da yadda ake yin Ƙuli-ƙuli, ku biyo mu a sannu domin mu koya tare……

Ko kun san ƙuli-ƙuli abincin yara ne? ko ince yara na son ƙuli-ƙuli, kuma ana iya sarrafa shi ta hanyar yin garin ƙuli-ƙuli sannan ya zama ingredients ɗin abincin kowa.

Abubuwan Buƙata:

 1. Gyaɗa
 2. Gishiri
 3. Citta
 4. Barkono
 5. Sinadarin ɗanɗano
 6. Sugar

Yadda Ake Haɗawa:

 1. A soya gyaɗa sama-sama sai a ɓarza ta, a tabbatar an tsince an ɓarza (babu mai bori kwata-kwata).
 2. A fitar da baƙin gyaɗa, domin tana saka ɗaci.
 3. Sai ka kai, a markaɗa kar a zuba ruwa kamar ƙullin gyaɗa (peanut butter)
 4. A jiqa.
 5. A tsince gyaɗa, a cire mai bori sannan a cire baɗin gyaɗar sai a soyata sama-sama karta ƙone
 6. A markaɗa gyaɗa ɗan gishiri, citta ko in mai sugar za a yi sai an ɗan saka sugar.
 7. A tace ruwan tsamiya a bar shi ya kwanta, sai a juye a abu mai kyau.
 8. Bayan an markaɗa gyaɗa, sai a saka ta a cikin kwano mai zurfi a zuba wannan ruwan tsamiya kaɗan a yi ta juyawa da muciya ko cokalin katako har sai an ga mai ya fara fitowa.
 9. Sannan za a ga gasarar tana curewa ko ince yana dunƙulewa. Sai a tsiyaye mai, sannan a cura ƙullin a soya ta.

Domin koyon Yadda Ake Yin Daƙuwa danna nan

Domin koyon Yadda Ake Kunun Gyaɗa danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Yin Kantun Ghana
Labarin na GabaYadda AkeTherapeutic Food (abincin yara)