Barkanmu da sake kasancewa acikin shirinmu na GIRKE GIRKEN WikiHausa wanda muke koyarda ƙayatattun abinci namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tareda bayani akan lafiyarsu cikin harshen hausa a saukake tare dani Hafsat Shettimah.
A yau zamu koyar da yadda ake Abinci yara (therapeutic food); ku biyoni a sannu domin mu koya tare……
Ko kun san:- Yara masu cutar yunwa (tamowa) idan ana basu wannan zai kara musu kuzari da kumara a jiki.
Abubuwan Buƙata
- Gyaɗa (kofi biyu)
- Waken suya (kofi biyu)
- Dawa (kofi shida)
- Siga
- Madara (in ana buƙata).
Yadda Ake Haɗawa
- A soya Gyaɗa a busheta sannan a niƙa
- A soya Waken (Soya Beans) shima a niƙa
- Dawa itama a soyata sannan a niƙa
- Cikin roba mai kyau a haɗa dukkanin garin (Wake Soya, Dawa da kuma Gyaɗa) a juya da kyau sai a sami leda mai kyau a juye a cikin sannan a saka a roba mai murfi a rufe. Duk sanda za’ayi sai a ɗiba.
Yadda ake haɗa kunun
- A ɗora tukunya mai zurfi sannan azuba ruwan zafi kaɗan yadda zai isa (kamar talge).
- A ɗan kofi ko roba a ɗebi garin kunun yara sai azuba ruwa a cikin ɗan kaɗan a dama.
- Idan ruwan ya tausa sai azuba wannan gasarar kunun a cikin ruwan ayita juyawa har sai yayi kauri
- Za’a iya saka madara domin ƙarin daɗi kuma za’a iya sha a haka.
Domin sanin Yadda Ake Gasarar Gyaɗa (Peanut Butter) danna koren rubutun nan.