Yadda Ake Gasarar Gyaɗa (Peanut Butter)

0
1151

Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na Girke-Girken WikiHausa, wanda muke koyar da ƙayatattun abinci namu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shettimah.

A yau za mu koyar da yadda ake yin gasarar gyaɗa (peanut butter) ku biyo ni a sannu domin mu koya tare.

Ko kun san gyaɗa na ɗauke da sinadarai masu gina jiki, kamar protein, fiber, vitamin E, potassium, magnesium, za mu iya sarrafa gasarar gyaɗa waje abinci kala-kala, kamar; kunun gyaɗa, sandwich ko kuma ana iya ci da biredi da sauransu.

Abubuwan Buƙata:

  1. Gyaɗa mara ɓawo [kofi ɗaya]
  2. Gishiri
  3. Barkono rabin ƙaramin chokali
  4. Chitta rabin kwatan ƙaramin chokali 1/3.

Yadda Ake Haɗawa

  1. A cikin tukunya mai zurfi a zuba gyaɗa a soya ta, har sai ta yi kalar ƙasa (wato golden brown)
  2. Sai a juye gyaɗar a matankaɗi, a cire ɓawon jikin, sannan a bakace, har sai ta fita tas.
  3. A zuba kayan ƙamshi a ciki, sannan a markaɗa. Amma kar a saka ruwa
  4. Za a iya ci da biredi, ko yalon Bello, sannan ana iya yin kwaɗo da shi, ko kunun gyaɗa nau’o’in abinci masu lafiya. NOTE:- za a iya kunun da shi.

Danna koren rubutu domin karanta Yadda Ake Dafaffiyar Gyaɗa da Yadda ake Gyaɗa Marau-marau

labarin da ya wuceYadda Ake Haɗa Sandwich kebab
Labarin na GabaYadda Ake Yogurt