A yau za mu koyi yadda ake ajiye kayan miya tsawon shekara.
Abubuwan da ake bukata:
- TUMATUR
- ATTARUHU
- TATTASAI
Yadda ake yi shi ne:
- Da farko za a samu kwalabar bama wato mayonnaise amma a tabbata akwai wani kwali a saman murfin
- Za a wanke a gyara su tsaf a markaɗa su
- Za a samu colander babba a zuba kayan miyan a daura a kan bokiti domin ruwan kayan miyan ya tsane ko ya ragu saboda samun sauki wajen dahuwar ruwan zai tsotse da wuri
- Sai a zuba kayan miyar a bar shi yai ta dahuwa
- A ringa juyawa lokaci zuwa lokaci har sai ruwan kayan miyan ya gama ƙonewa baki ɗaya
- Su sai a ringa ɗiba a kan wutar, kada a sauke
- A ringa diba ana zubawa a cikin kwalbar ana jijjigawa domin yai kasa sosai kada a bar wata iska a ciki, har sai ya yi ciki.
- A danna da ludayi sosai ya cika bam sai a ɗauki murfin a rufe sosai
- Haka za a yi ta yi har a gama.
- Za a daura ruwa a wata tukunyar a dafa shi, amma kada ya tafasa sai a zuba kwalaban a cikin baho a kwara ruwan zafin a rufe kmar 1 hour sai a cire su a ajiye a kitchen ko cikin drowers ko a kasa ma duk dai inda ake so a ajiye