Abubuwan da ake bukata domin hada Rice Butter Cookies cikin sauki.
- fulawar shinkafa 1 cup
- Butter 4 tablespoon
- Baking powder ½ teaspoon
- Bi- carbonate soda ½ teaspoon
- Natmeg da cinnamon ½ teaspoon each
- ƙwai guda 1
- strawberry ko cherry idan ana buƙata.
Domibn sanin yadda ake miyar karkashi da kubewa danna nan
Yadda Ake Haɗawa
- A haɗa komai cikin roba a murzashi da kyau.
- sai a sami rolling pin da board a murza a yanka zuwa shape ɗin da ake so za’a iya yi mishi ado da cherry yankakku ko kuma strawberry a ɗora sa sama bayan an yanka zuwa shape ɗin da akeso .
- A ɗora akan farantin gashi a gasa na minti 10 – 15 a temperature 110c – 115c.
Domin karanta Yadda Ake Rice Cocktail Bites Cikin Sauki Danna nan