Egg muffins abinci ne da ake yin sa daga ƙwai; ƙwai na da matuƙar amfani. Egg muffin yana da daɗi a karin kumallo ko tarar baƙi.
Abubuwan da ake buƙata
- Ƙwai Dafaffe
- Dankali Turawa
- Dafaffafen nama
- Koren tattasai
- Tarugu
- Albasa
- Maggi
- Curry da thyme
- Gishiri kaɗan
- Butter Ko mai
- Baking power
Yanda ake haɗawa
- A yayyanka nama, albasa, taruhu da dafaffen ƙwan. Amma kar a sa dafaffen dankali
- A kawo Curry da thyme kaɗan a sa, A ɗauko Maggi na ruwa a sa (za a iya amfani da su ne normal Maggi). Sai a juye a ajiye a gefe
- A sami ƙaramin kwano a fasa kwai, a ciki sai a sa baking powder sai gishiri kaɗan Sai a kara juyashi
- A ɗauko muffin pan a shafa mishi mai ko butter
- Sannan ki ɗauko Dafaffen dankali (yankakke) kisa a ciki
- Sai a sa a cikin oven a gasa, har sai ya gasu (ya zama golden brown)
- Za a iya ci haka ko kuma a haɗa shi da soyayyen dankali Turawa. A ci daɗi lafiya
Domin sanin yadda ake potato balls danna nan