A yau na zo mana da yadda ake haɗa dambun nama; na kaza ko dai na jan nama. Danbun nama na daga cikin abincin da ake samarwa daga nama. Yana da matuƙar daɗi.
Abubuwan da ake buƙata
- Nama/kaza
- Taruhu
- Albasa
- Tafarnuwa
- Seasoning
- Man gyaɗa
Yadda ake haɗawa
- Da farko za a wanke nama, ko kaza, a zuba cikin tukunya, a zuba albasa da taruhu da tafarnuwa.
- A ɗora a wuta, a bar shi, ya yi ta dahuwa kamar awa 4/5 yana dahuwa.
- Idan an sauke, sai a raba shi da ƙashi da kitsensa, ko fata duka, a cire a mayar da tsokar a sa muciya a tuƙe shi, a sa seasoning da spices.
- Sai a zuba man gyaɗa har ya rufe naman a soya. Ba za a ɗaga ba, a na yi ana juya shi har ya yi.
- Sai a kwashe a saka a cikin abun tata a matse man. A tabbatar ba sauran mai, sai a zuba cikin sieve ko colander. A ci lafiya
Domin sanin Yadda Ake Egg Muffin danna nan