-
Naman kaza: Naman kaza da sauran danginsa suna hana barci mai dadi, matukar aka ci kafin barci. Wannan na faruwa ne, saboda narkewar abinci a jikin dan Adam na ɗaukar lokaci ya yin barci. A maimakon ɗan Adam ya yi barci mai daɗi, jikinsa zai maida hankali ne wajen narkar da abincin.
-
Kayan kwalam masu sukari: Wannan a bayyane yake, duk da mutane da yawa na cin irin wadannan abincin kafin su kwanta. Wannan ba abin da ya dace ba ne, don kuwa suna ɗaukar lokaci kafin su narke a jiki. A maimakon jikin mutum ya samu sauki da hutu yayin kwanciyar barcin, sai ya yi ta kokarin narkar da abincin wanda hakan zai hana barci mai nagarta.
-
Shayin Coffee: Duk da kuwa abin sha ne, yana ɗaya daga cikin abubuwan da ya kamata a guda kafin a kwanta. Wannan kuwa za a iya danganta shi ne da sinadarin ‘caffeine’ da ke ciki wanda ke hana barci.
Amma kuma, idan mutum na da burin kin barci, toh zai iya shan coffee don wannan aikin. Abin kiyayewa a nan kawai shi ne, kada ya zama mutum ya saba, don akwai matsalolin da ke akwai dangane da sabo da shan sinadarin caffeine.
-
Abinci mai yaji: Duk yadda mutum ke son abinci mai yaji, zai fi idan aka ci da safe ko da rana amma a kiyaye da dare. Abinci mai yaji kan jawo tashin zuciya, idan aka ci da dare kuma hakan yakan hana nagartaccen barci.
-
Abinci mai maiƙo: A shawarce abinci mai maiko abin gudu ne da daddare ,don samun lafiya mai inganci. Maiƙon dake ƙunshe a abincin nasa ciki ya fitar da ‘acid’ wanda yake kawo tashin zuciya. A don haka ne idan ana bukatar barci mai nagarta tare da gudun tashin zuciya da safe, sai a guji abinci mai maiko da dare.