Pancake abinci mai sauƙin sarrafawa kuma na karin kummalo ko kuma domin yara ‘yan makaranta ana iya cin pancake da lemo ko madara ko shayi.
ABUBUWAN BUƘATA
- fulawar shinkafa 1 ½ kofi ɗaya da rabi
- Madarar ruwa rabin kofi 1 ½ cup
- kwai 2
- Baking powder (baƙin hoda) ½ teaspoon
- sugar ½ kofi
- flavour (vanilla flavour) 1 teaspoon.
- Bota (butter) ¼ cup
- Dafaffiyar shinkafa kofi ɗaya 1 cup.
Yadda Ake Haɗawa
Domin karanta cikakken bayani akan Mene Ne Abinci A Lafiyance? danna nan.
- A haɗa dry ingridients cikin roba mai tsafta (fulawa, baƙin hoda).
- A cikin wata roba mai zurfi a sa bota da siga ayita juyawa har sai yayi fari.
- A fasa kwai a zuba ana juyawa.
- Bayan nan sai a zuba madara, filabo a juya.
- A ɗauko fulawa mai baƙin hoda a zuba a juya da kyau sannan a zuba dahon shinkafa.
- A sami abun gashi mara kamu (non- sticky frying pan) A shafa mai sai a zuba gasarar pancake idan ya gasu sai a juya ɗayan ɓarin shima ya gasu.
- Haka za’a yi tayi har a gama da gasarar.
Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Farfesun Kayan Ciki A Sauƙaƙe danna nan.