Barkan mu da kasancewa a fannin girke-girkenmu na WikiHausa; A yau za mu koyi yadda ake farfesun kayan ciki a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shettima.
Farfesun kayan ciki na mutum 3-4
Abin da ake buƙata
- Kayan ciki (Na rago, shanu, ko akuya)
- Albasa yankakken matsakaita 2s
- Jajjagaggen Tumatir matsakaita 1
- Attaruhu Jajjagaggen (to taste)
- Jajjagaggen Tattasai madaidaita 2
- Sinadarin ɗanɗano (Maggi, Knorr, onga, etc.)
- Sinadarin ƙamshi (Garlic, gyaɗar miya, curry, etc)
- Ruwa kofi 3 da rabi
Yadda ake haɗawa
- A wanke kayan ciki sosai su, fita tsaf.
- Cikin tukunya mai zurfi a zuba kayan ciki da rabin albasa, kayan ƙamshi da kofi biyu ruwa, da Sinadarin ɗanɗano.
- Idan ya dahu sai a saka markaɗaɗɗen kayan miya da saura kayan ɗanɗano, a ɗan bar shi kamar minti 4-5, sai a juye raguwar ruwa a bar shi ya ci gaba da dahuwa na minti 10-15.
Domin koyan Yadda ake Farfesun Ganda na musamman danna wannan koren rubutun.