Yadda Ake Miyar Kuka

1
1539

Ganyen kuka wanda da ita ake miyar kuka, na da matuƙar amfani ga lafiyar ɗan Adam. Tana ɗauke da sinadarai da dama, waɗanda suka haɗa da ‘Vitamin C’, ‘Vitamin A’, ‘Beta Carotene’, ‘Potassium’, ‘Calcium’ da sauransu da dama.

Waɗannan Sinadarai kuma na taimakawa wajen magance wasu matsaloli da cututuka kamar su tari, tsutsar ciki, ciwon ƙoda, ciwon asthma, sanyin dake taruwa a ƙirji da sauransu.

Abubuwan da ake buƙata

Kuka
Attaruhu
Daddawa
Albasa
Bandar kifi
Nama
Magi
Man ja

Yadda ake haɗawa

1. Da farko za a ɗora ruwa a wanke nama, sai a yayyanka masa albasa da gishiri kadan. Sannan a rufe ya yi ta dahuwa har sai naman ya yi laushi sai a sauke a ajiye a gefe.

2. A ƙara ruwa kaɗan a kan silalen romon naman, sannan a yayyanka albasa sai a daka daddawa a zuba da jajjagen attaruhu mai tafarnuwa.

3. A wanke bandar kifi a zuba. Su yi ta tafasa har sai bandar ta dahu, sannan a zuba magi da manja a rufe su ƙara tafasa.

4. Bayan haka, sai a zuba kuka kaɗan, a riƙa kaɗawa ko da maburgi ko cokali domin kada a samu gudaji a ciki. Sai a ɗan rufe bayan ya ɗan tafasa sai a sauke.

Domin sanin Yadda Ake Fruit Salad danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Fruit Salad
Labarin na GabaYadda Ake Peppered Chicken
Khadija Yusha'u (Amira)
Khadija Yusha'u (Amira) Babbar ɗalibar Addini ce, wacce ta karanci abin ci da lafiyar sa (Food and Nutrition) da kuma ƙwararriyar mai haɗa abin ci da kuma koyar da aikin hannu.

SHARHI ƊAYA

  1. Assalamualaikum warahamtullahi wabarkatuhu,sunan malama safina,barka da warkahaka.dafatan kinan lafy ko Kuma Kuna Joshi lady da iyali gidanku lafy,na zo yada ake hadu abubuwa abinci kala kala Kuma suna hanfane garene sosai.