Yadda Ake Farfesun Dankalin Turawa Da Kaza

0
859

A yau za mu koyi yadda ake farfesun dankalin Turawa da kaza.

Abubuwan da ake buƙata

 • Kaza
 • Dankalin Turawa
 • Karas
 • Curry
 • Maggi,
 • Thyme
 • Tattasai
 • Tumatur

Yadda ake haɗawa:

 1. A fere dankali a yanka ƙanana,
 2. Sai a wanke kaza a sulala ta da maggi, curry, gishiri, thyme, sai a jajjaga tattasai, da tumatur
 3. Idan ya sulala, sai a zuba yankakken karas, a zuba dankalin shi ma, a juya har zuwa lokacin da zai yi, Wannan girkin an fi yi da safe domin ai breakfast da shi.

Domin sanin yadda ake creepes da vegitable danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Yin Crepes Da Vegetable
Labarin na GabaYadda Ake Yin Alalan Shinkafa
Khadija Yusha'u (Amira) Babbar ɗalibar Addini ce, wacce ta karanci abin ci da lafiyar sa (Food and Nutrition) da kuma ƙwararriyar mai haɗa abin ci da kuma koyar da aikin hannu.