A yau, za mu koyi yadda ake peppered chicken; Peppered chicken abinci ne da ake yin sa daga kaza, yana da matuƙar daɗi a wajen ci, musamman ma idan aka kula da tsaftar abubuwan haɗawar.
Abubuwan da ake buƙata
▪Chicken/Kaza
▪Onions
▪Red pepper
▪Green pepper
▪2 Chilli pepper
▪Soy sauce
▪pinch of Tumeric
▪Curry
▪Coriander powder
▪Garam masala
▪parsley
▪Maggie
▪Salt
▪Dried ginger
▪Oil
Yadda ake haɗawa
- A dafa nama tare da attarugu, Maggi, albasa, gishiri, citta, curry idan ya dahu sai a sauke a soya ta a mai.
- A zuba mai a cikin kasko sai a zuba yankakkiyar albasa a ciki.
- Sai a ɗan motsa kaɗan a sa Maggi, coriander powder, garam masala, red pepper, chilli pepper, turmeric, curry, soy sauce.
- A ɗan motsa kaɗan, sai a zuba kazar a ciki, a ci gaba da juyawa har jajjagen ya shiga ko’ina na jikin nama.
- Bayan sauce in ta kama nama, ko’ina ya ji sai a zuba green pepper da parsley a ɗan juya.
Domin sanin Yadda Ake Miyar Kuka danna nan