Apple Peanut Butter Sandwich
Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa, wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare. Tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shettimah. A yau zamu koyar da yadda ake apple griiled butter sandwich. Ku biyo ni a sannu domin mu koya tare.
Abubuwan da ake Buƙata:
- Tufa (apple) a yanka sala-sala
- Peanut butter (gasarar gyaɗa)
- Biredi yanka 4
- Cinnamon (kirfa) ½ cokali
- Bota cokali 1
Yadda Ake Haɗawa
- A cakuɗa tufa da siga da kirfa sai a jiye a gefe.
- A ɗauko biredi a shafa masa wannan peanut butter (gasarar gyaɗa) a ɓari ɗaya sai a jera wannan tufa mai siga da kirfa sai a rufe da wani biredin.
- A kasko mai matsakaicin zafi a shafa butter, sai a ɗora biredin a gasa ko wani ɓangare kamar na minti biyu ko kuma idan ya yi kalar ƙasa (golden brown).
Domin koyar Yadda Ake Kunun Gyada danna wannan koren rubutun.