Yadda Ake Yam Ball (Ƙwallon Doya)

0
2671

‘Yar uwa barkan mu da wannan lokaci a cikin wannan shiri mai albarka da fatan kuna cikin ƙoshin lafiya. Allah ya sa mu dace.

Makon da ya gabata ne muka tattauna kan yadda ake soyayyen dankalin Hausa na musamman da kuma yadda ake miyar kwai.

A wannan makon kuma shirin namu zai karkata domin kawo muku yadda ake yam ball.

Da yawa mata suna son su yi yam ball, sai su ga yana sha musu mai, ko kuma ya rika wargajewa, toh ga yadda za ki yi shi, ya yi kyau, ba tare da ya ba ki matsala ba.

 

Kayan da ake buƙata:

Yam

Onion

Peppe

Spices

Egg

Maggi

Salt

Yadda ake yi:

Da farko dai uwargida za ki fere doyarki, ki yanka ta manya, sai ki wanke ta tsaf, kisa ta a pot da ɗan ruwa daidai misali, ki zuba salt kaɗan, sai ki bar ta ta dahu sosai yadda ba za ta ba ki wahalar dakawa ba.

Idan ta dahu, sai ki dakko tsaftataccen turminki, da raɓaryarki, ki riƙa tsamo doyar kina sa ta a turmi kina daka ta, in ta daku sosai, sai ki kwashe a mazubi mai tsafta, amma fa wajen dakawar kada ta yi luƙwi kamar dakan sakwara, kuma kada ki yi sama-sama don irin shi ne ke jawowa ta rushe a cikin mai, sai a kula saboda a yi abin yadda zai ƙayatar sosai, dama kin riga kin daka taruhu da onion kin sa kayan ƙamshinki da maggi da gishiri, sai ki ɗan sa ruwa kaɗan, don su narke, sai ki zuba a kan dakakkiyar yam ɗinki, ki juya sosai in kuma kin ga bai juyu ba, sai ki mayar turmi ki bubbuga har ya bugu sosai.

Bayan kin kammala dakan kin kwashe, sai ki riƙa dunƙula shi kamar ball(kwallo), Sai ki kaɗa ƙwai, ki sa mishi albasa wadda kika yanka ƙanana, ki zuba salt, sai ki juya ki yanka wa mai albasa, ki ɗora a wuta, ta soyu, sai ki dinga ɗauko wannan dunƙulen yam din ki rinƙa tsomawa a cikin wannan ruwan ƙwan din, sai ki sa su cikin soyayyen man nan, in ya yi, zai yi brown shi kenan sai ki tsame

A ci lafiya.

Uwar gida ana shirin namu zai dakata sai wani makon, da yardar Allah za ku ji mu ɗauke da ci gaban shirin.

labarin da ya wuceYadda Ake Soyayyen Dankalin Hausa Da Miyar Ƙwai
Labarin na GabaYadda Ake Kunun Gyaɗa