Author: Ismail Muhammad Sani

  • Yadda Ake Ƙosan Dankali Mai Haɗe Da Nama

    Yadda Ake Ƙosan Dankali Mai Haɗe Da Nama

    • Dankali
    • Nama
    • Kwai
    • Attaruhu
    • Albasa
    • Maggi
    • Gishiri
    • Man gyaɗa
    • Fulawa ko garin busashen buredi

    *YADDA AKE HAƊAWA*

    Da farko ki wanke nama ki zuba a tukunya sai ki zuba maggi da gishiri ki tafasa sai ki kwashe ki zuba a turmi ki jajjaga tare da albasa da attaruhu idan ya yi laushi sai ki kwashe a kwano ko roba. Sannan ki dawo kan dankalin turawa ki tafasa ya yi laushi sai ki murmushe shi ko kuma ki jajjaga a turmi sai ki kwashe shi a cikin kwanon da kika kwashe naman da kika jajjaga, sai ki ɗauko ƙwai ɗanye ki fasa a kai, ki zuba fulawa ko garin busasshen buredi a ciki, ki sa gishiri da maggi ki juya sosai. ki ɗauki farantin suya ki zuba man gyaɗa ki ɗora a kan wuta ki dinga ɗiba kina zuba wa a cikin man gyaɗa mai zafi idan ya soyu za ki ga ya yi brown sai ki kwashe. Ki yi wa Oga ya yi breakfast da shi.

    ƘOSAN DANKALI 

    *KAYAN BUKATA*

    • Dankalin turawa
    • Nama
    • Fulawa
    • Kwai
    • Albasa
    • Attarugu
    • Gishiri
    • Maggi
    • Man gyada

    *YADDA AKE YI*

    Ki jajjaga albasa da attaruhu ki kwashe a kwano ko roba sai ki ɗauki dankali ki tafasa ki zuba a turmi ki daka shi amma kar ya yi laushi sai ki kwashe a cikin kwanon da kika zuba jajjagen attaruhu da albasa ki tafasa nama shi ma ki daka a turmi duk ki haɗa da sauran kayan haɗin ki juya, sai ki dinga mulmulawa kina tsomawa a ruwan ƙwai ki juya shi a cikin fulawa ki jefa a cikin man gyaɗa mai zafi ki soya, akwai daɗi matuƙa…

    Don karanta Yadda Ake Plantain Pie danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Ake Yam Ball (Ƙwallon Doya)

    Yadda Ake Yam Ball (Ƙwallon Doya)

    ‘Yar uwa barkan mu da wannan lokaci a cikin wannan shiri mai albarka da fatan kuna cikin ƙoshin lafiya. Allah ya sa mu dace.

    Makon da ya gabata ne muka tattauna kan yadda ake soyayyen dankalin Hausa na musamman da kuma yadda ake miyar kwai.

    A wannan makon kuma shirin namu zai karkata domin kawo muku yadda ake yam ball.

    Da yawa mata suna son su yi yam ball, sai su ga yana sha musu mai, ko kuma ya rika wargajewa, toh ga yadda za ki yi shi, ya yi kyau, ba tare da ya ba ki matsala ba.

     

    Kayan da ake buƙata:

    Yam

    Onion

    Peppe

    Spices

    Egg

    Maggi

    Salt

    Yadda ake yi:

    Da farko dai uwargida za ki fere doyarki, ki yanka ta manya, sai ki wanke ta tsaf, kisa ta a pot da ɗan ruwa daidai misali, ki zuba salt kaɗan, sai ki bar ta ta dahu sosai yadda ba za ta ba ki wahalar dakawa ba.

    Idan ta dahu, sai ki dakko tsaftataccen turminki, da raɓaryarki, ki riƙa tsamo doyar kina sa ta a turmi kina daka ta, in ta daku sosai, sai ki kwashe a mazubi mai tsafta, amma fa wajen dakawar kada ta yi luƙwi kamar dakan sakwara, kuma kada ki yi sama-sama don irin shi ne ke jawowa ta rushe a cikin mai, sai a kula saboda a yi abin yadda zai ƙayatar sosai, dama kin riga kin daka taruhu da onion kin sa kayan ƙamshinki da maggi da gishiri, sai ki ɗan sa ruwa kaɗan, don su narke, sai ki zuba a kan dakakkiyar yam ɗinki, ki juya sosai in kuma kin ga bai juyu ba, sai ki mayar turmi ki bubbuga har ya bugu sosai.

    Bayan kin kammala dakan kin kwashe, sai ki riƙa dunƙula shi kamar ball(kwallo), Sai ki kaɗa ƙwai, ki sa mishi albasa wadda kika yanka ƙanana, ki zuba salt, sai ki juya ki yanka wa mai albasa, ki ɗora a wuta, ta soyu, sai ki dinga ɗauko wannan dunƙulen yam din ki rinƙa tsomawa a cikin wannan ruwan ƙwan din, sai ki sa su cikin soyayyen man nan, in ya yi, zai yi brown shi kenan sai ki tsame

    A ci lafiya.

    Uwar gida ana shirin namu zai dakata sai wani makon, da yardar Allah za ku ji mu ɗauke da ci gaban shirin.

  • Yadda Ake Ƙosan Dankali Mai Haɗe Da Nama

    Yadda Ake Ƙosan Dankali Mai Haɗe Da Nama

    KAYAN HAƊI

    • Dankali
    • Nama
    • Kwai
    • Attaruhu
    • Albasa
    • Maggi
    • Gishiri
    • Man gyaɗa
    • Fulawa ko garin busashen buredi

    *YADDA AKE HAƊAWA*

    Da farko ki wanke nama ki zuba a tukunya, sai ki zuba maggi da gishiri, ki tafasa sai ki kwashe ki zuba a turmi ki jajjaga tare da albasa da attaruhu, idan ya yi laushi, sai ki kwashe a kwano ko roba, sannan ki dawo ɗan dankalin Turawa ki tafasa ya yi laushi, sai ki murmushe shi ko kuma ki jajjaga a turmi, sai ki kwashe shi a cikin kwanon da kika kwashe naman da kika jajjaga, sai ki ɗauko ƙwai ɗanye ki fasa a kai, ki zuba fulawa ko garin busasshen buredi a ciki, ki sa gishiri da maggi ki juya sosai, ki ɗauki farantin suya ki zuba man gyaɗa ki ɗora a kan wuta ki dinga ɗiba kina zubawa a cikin man gyaɗa mai zafi idan ya soyu za ki ga ya yi brown sai ki kwashe ki yi wa Oga ya yi breakfast da shi.

    ƘOSAN DANKALI

    *KAYAN BUƘATA*

    • Dankalin Turawa
    • Nama
    • Fulawa
    • Kwai
    • Albasa
    • Attaruhu
    • Gishiri
    • Maggi
    • Man gyaɗa

    *YADDA AKE YI*

    Ki jajjaga albasa da attaruhu, ki kwashe a kwano ko roba, sai ki ɗauki dankali, ki tafasa ki zuba a turmi ki daka shi, amma kar ya yi laushi sai ki kwashe a cikin kwanon da kika zuba jajjagen attaruhu da albasa, ki tafasa nama shi ma ki daka a turmi, duk ki hada da sauran kayan haɗin ki juya, sai ki dinga mulmulawa kina tsomawa a ruwan ƙwai, ki juya shi a cikin fulawa ki jefa a cikin man gyaɗa mai zafi ki soya , akwai daɗi matuƙa.

  • Yadda Ake Kulle Post Ɗin Da Bai Dace A Gani  A Facebook Ba (Hide Post)

    Yadda Ake Kulle Post Ɗin Da Bai Dace A Gani A Facebook Ba (Hide Post)

     

    Yau za mu koyar da yadda za ka goge (share) post din da ba ka son ganin shi a Facebook. Sau da yawa mutane suna turo hotuna ko bidiyo waɗanda ba su dace ka kalle su ba kuma ka rasa yadda za kai ka goge su.

    Ta yaya za ka ɓoye ko ka goge post din(hide)?

    1. Ka shiga Facebook ɗin ka sai ka je daidai post ɗin da kake son gogewa (hide), daga sama ɓangaren hannu dama za ka ga ɗugo guda uku a jere, kamar haka, sai ka taɓa su

    2. Bayan ka taɓa su, za ka ga wasu rubutu sun fito kamar haka:

    3. Sai ka taɓa inda ka rubuta “I don’t want to see this” za ka ga wasu rubutu sun fito kamar haka:

     

    4. Sai ka taɓa inda aka rubuta “hide post”, bayan ka taɓa shi kenan za ka daina gani wannan post din.

    Idan kuma wanda ya yi wannan post ɗin dama ya saba turo abubuwa marasa ma’ana, za ka iya kulle post ɗinsa duka, ta yadda ba za ka ƙara ganin wani post ɗinsa a cikin account ɗinka na Facebook ba, ka kula sosai bayan inda aka rubuta “hide post” akwai wasu rubutun a ƙasa, kula sosai za ka ga inda aka rubuta “hide all form Ibrahim Ali”

    Idan ka taɓa wajen shi kenan duk sanda ya yi post ba za ka rika gani ba. (Ku kula inda aka rubuta Ibrahim Ali shi yake nuna shi ne ya yi post din)

    Kar ku ji komai wajen yin tambaya a kan abin da ba ku gane ba. Ku sani, saboda ku muke yi.

  • Yadda Ake Cire Auto Download A WhatsApp

    Yadda Ake Cire Auto Download A WhatsApp

    Barkam mu da kasancewa da ku a wannan gida mai albarka WikiHausa.com.ng

    Yau zamu koyar da ‘yan uwa yadda ake cire auto download a WhatsApp. Sau da yawa za ku samu WhatsApp yana sauke muku hotuna bidiyo a wayarku ba tare da izininku ba, kuma hotunan sun haɗa da wanda ya kamata da kuma wadanda bai kamata ba.

    Ta yaya zan dakatar da shigowar hotuna ko bidiyo daga WhatsApp ɗina?

    Ka bi waɗannan sauƙaƙan hanyoyin don cire WhatsApp auto download.

    1. Ku shiga WhatsApp ɗinku daga sama, za ku ga wasu ɗigo guda uku, kamar yadda wannan hotan na ƙasa ya nuna. Sai ku taɓa su.

    2. Za ku ga wani waje da aka rubuta setting, sai Ku Shiga.

    3. Sai ku shiga inda aka rubuta “Data And Storage Usage” kamar yadda wannan hotan ya nuna

    4. Za ku ga wani waje an yi tik a kan wani ɗan akwati kamar haka.

    5. Sai ku tattaɓa su, za ku ga makin ɗin ya fita kamar haka.

    Shi kenan WhatsApp ɗinku ba zai ƙara yi muku auto download ba.

    Kar ku manta, duk sanda kuka goge WhatsApp dinku, to tabbas settings ɗin ya wargatse. Sai kun sake saitawa.

    Kar ku ji komai wajen tambaya ko neman ƙarin bayani, ku sani saboda ku muke yi.