Yadda Ake Caramelized Onion Grilled Cheese Sandwich

0
967

Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shettimah. A yau za mu koyar da Yadda ake caramelized onion grilled cheese sandwich. ku biyo ni a sannu domin mu koya tare.

Caramelized onion grilled cheese sandwich

Abubuwan buƙata:

  1. Butter chokali 3
  2. Albasa yankakiya guda 1
  3. Masora dakakke (black pepper)½  cokali
  4. Cheddar cheese slice
  5. Bbq sauce chokali biyu-uku

Yadda ake haɗawa

  1. A ɗora kasko a matsakaiciyar wuta, sai a narka butter a zuba albasa a soya, har sai ta soyu, a saka ɗan gishiri, sinadarin ɗanɗano da attaruhu da kuma bbq sauce.
  2. A ɗauko biredi a zuba wannan albasa, a ɗora cheese gudu ɗaya (falle ɗaya) sannan a rufe da wani biredin.
  3. Sai a saka a cikin toaster a gasa sannan a biyu. (diagonally)
labarin da ya wuceYadda Ake Banana Nutella Sandwish
Labarin na GabaYadda Ake Egg French Toast