A yau za mu koyi yadda ake pride gish & irish potato,
Abubuwan da ake haɗawa
- Kifi
- Dankali
- Curry
- Maggi
- Mai
- Attaruhu
- Kayan ƙamshi
- Kwai
- Albasa
Yadda ake haɗawa
- A fasa kwai a ajiye, sai a dafa dankali, in ya dahu sai a sauke, a ɗauko kifi da kayan ƙamshi da attaruhu, a daka su a turmi.
- Bayan an gama, sai a soya su a ɗauko wannan dankalin da aka dafa, a zuba a turmi a daddaka shi.
- Sai a zuba a wannan kwano da aka fasa ƙwai a ciki, a haɗa da wannan kifin da dankalin, a cakuɗa su, sai a ɗora mai a kan wuta, ki rinƙa mulmulawa ana soyawa har a gama.
Domin sanin yadda kunun aya danna nan