A yau za mu koyi yadda ake kunun kus-kus, kunun kuskus na ɗaya daga cikin abin sha mai daɗi da riƙon ciki. Kasancewar yana ɗauke da madara a cikinsa.
Abubuwan da ake buƙata:
- Couscous
- Sikari ko zuma
- Madara
- Tufa
- Ayaba
- Flavour na banila
Yadda ake haɗawa
- A sami madarar gari ko ta ruwa,
- Sai a kwaɓa ta da ruwa, ta yi tsululu sai a ɗora a kan wuta,
- Idan ta tafaso, sai a kawo kus-kus ɗin a zuba a ciki, a ringa juyawa domin kada ya dunƙule.
- Sannan idan an zuba, iya yawan da ake so, sai a ci gaba da juyawa har zuwa minti biyar.
- Idan ya dahu kuma, kaurin ya yi, sai a sauke daga kan wuta a zuba sikari,
- A yanka tufa da ayaba a saka sikari ko kuma zuma duk wanda ake so,
- Sannan a ƙara madara, a zuba flavour mai ƙamshin vanilla a juya.
Domin sanin yadda ake kunun aya danna nan