Aya tana ƙara ƙarfin garkuwar jiki ga mai yawan amfani da ita. Aya tana inganta yanayin da mutum ke ciki, tana tsawaita ƙuruciya, tana ƙarfafa yanayin gudanar jini, sannan tana ƙara kuzari na zahiri.
Haka kuma Aya tana da amfani ga sha’anin da ya shafi ciki da hanji, tana ɗauke da sinadarin dake hana cushewar ciki da kuma kumburi. Har ila yau, tana taimakawa wajen rage sinadarin kwalestaral mara kyau a cikin jini.
Abubuwan da ake buƙata
- Aya
- Suga
- Ɗanyar citta
- Flavour
- Kwakwa
- Madarar ruwa
- Dabino
Yadda ake haɗawa
1. A jiƙa aya ta jiƙu, a wanke ta, a saka kwakwa 1 da dabino kamar 7 ko 10, da citta ɗanya ko busasshiya, sai a niƙa.
2. Sai a tace, a zuba madara a ciki, a sa suga da flavour a juya, a jefa ƙanƙara ko asa a fridge.
Domin sanin Yadda Ake Spicy Meat danna nan