Barkan mu da sake kasance a fannin girke-girkenmu na WikiHausa, za mu koyi yadda ake kunun alkama.
Kunun alkama dai yana da ruƙon ciki kuma yana da lafiya a jiki musamman a gurin masu ciwon siga, amma sai dai kada su yi amfani da suga wajen shan kunun.
Abubuwan Da Ake Buƙata
- Alkama
- Gyaɗa
- Sugar
- Citta
- Cardamon
- Ruwa
- Fulawa
- Nono ko tsamiya
Yadda Ake Haɗawa
- Ki gyara alkama ki wanke, ki sa ruwa a tukunya ki zuba alkama, cardamom, citta busasshe, ki bari ya tafasa; alkamar ki ya yi rabin nunar sa.
- Ki samu roba ki sa niƙaƙƙen gyaɗa da ruwa ki dama sai ki tace. Bayan alkama ta yi rabin dahuwarta ki sa tatacciyar gyaɗar, ki sa sugar yadda kike so. Ki bari alkaman ta nuna yadda ki ke so.
- Sai ki dama flour ki kaɗan a wani ƙaramin bowl, ki zuba a kan kunun, ki gauraya. Ki sauke bayan minti huɗu ko biyar.
- Sannan ki nemi rariya ki tace nono ko tsamiya sai ki zuba. Wasu a kan wuta suke zubawa wasu kuma sai bayan sun sauke, duk wadda kike so duk ɗaya ne.
Ƙarin bayani
Za ki iya saka kimba ko kanunfari a ciki, yana sa kunu ya ƙara ƙamshi sosai.
Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Shinkafa Da Miyar Attaruhu danna nan.