Yadda Ake Kunun Gyaɗa Mai Ayaba da Kwakwa

0
1373

Abubuwan da ake buƙata domin haɗa ƙunun gyada mai Ayaba da Kwakwa ba su da yawa; kunun gyada mai ayaba da kwakwa yana da matuƙar daɗi sosai musamman a ce an kula da tsafta a lokacin da ake haɗa sa.

Abubuwan Da Ake Buƙata:

  1. Kayan haɗi
  2. Gyaɗa
  3. Madara
  4. Ayaba
  5. Kwakwa
  6. Suga
  7. Shinkafar tuwo

Yadda Ake Haɗawa:

Ki samu gyaɗa, ki gyara ki wanke ki jiƙa, idan ta jiƙu, sai ki sabule ɓawan duka.
Ki samu shinkafar tuwo ki jiƙa, idan ta jiƙu, ki haɗa da gyadar ki markaɗa, sannan ki tace ki ɗora a kan wuta.
Ki ta juyawa saboda kar ya yi gudaji, idan yai kauri yadda kike buƙata, sai ki matsa lemon tsami ki sauke, idan ya ɗan sha iska.
Sai ki zuba a kofi ki sa madara da suga, dama kin goga kwakwa ki zuba a kai; sai ki yanka ayaba ita ma ki jera a sama, shi kenan sai sha.

Domin karanta Yadda Ake Kunun Kwakwa Ga Masu Ciwon Siga ko Yadda Ake Kunun Zaƙi danna koren rubutu.

labarin da ya wuceYadda ake Danbun Shinkafa
Labarin na GabaMutane Biyar Da Suka Yi kama Da Manzon Allah (S.A.W)