Yadda Ake Haɗa Groundnut, Rice, Sweet Potato Shake

0
1251

Barkanmu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abinci, namu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe tare da ni Hafsat Shettimah.

A yau za mu koyar da yadda ake yin groundnut, rice, sweet potato shake, ku biyo mu a sannu domin mu koya tare.

Ko kun san Gyaɗa na da sinadarin minerals kamar su: copper, manganese, potassium, calcium, iron, magnesium, zinc da kuma selenium wanda suke ƙara ƙarfin ƙashi da haƙori.

Abubuwan Buƙata

 1. Shinkafa ½ rabin kofi
 2. Gyaɗa ½ rabin kofi
 3. Dankalin Hausa
 4. Gyaɗa soyayyiya
 5. Siga
 6. Madara

Yadda ake haɗawa

 1. A wanke shinkafa a jiƙa ta, sai ta yi laushi
 2. A fere dankalin Hausa a yayyanka
 3. A soya gyaɗa a busar da ita
 4. Sai a hade gyaɗa, dankali da kuma jiƙaƙƙiyar shinkafa a markaɗa a tace da abun tata
 5. A raba ruwan gyaɗa biyu da aka ɗora a wuta har sai ya yi kauri (kamar kunun gyaɗa). Sai a sauke, a haɗe da ragowar ruwan gyaɗar a saka madara da siga. Za a iya ƙara ruwa daidai ƙaurin da ake so.
 6. Za a iya tace shi da rariya, idan ya yi gudaji-gudaji, sai a saka a fridge ya yi sanyi.
 7. Asha lafiya.
labarin da ya wuceYadda Ake Groundnut Sweet Potato Balls
Labarin na GabaMazajen Da Nana Khadija Ta Aura Kafin Manzon Allah (S.W.A)