Yadda Ake Groundnut Sweet Potato Balls

0
540
Ko kun san:- groundnut sweet potato balls na da saurin narkewa a jikin dan adam. Hakan yasa ya zama abinci mai kyau wurin yara da tsofaffi.

Abubuwan Buƙata

 1. Soyayyar gyada ¼ cup
 2. Dankalin hausa matsakaita
 3. Albasa a yanka kanana ko a jajjaga
 4. Curry ½ tablespoon
 5. Markadadden nama
 6. Sinadarin dandano
 7. Attaruhu guda biyar jajjagge
 8. Tafarnuwa
 9. Breadcrumbs 1 cup
 10. Kwai 3 (a fasa a kadashi)
 11. Man gyada na suya

Yadda ake hadawa

 1. A cikin kwano mai kyau a zuba dafaffiyar dankali sai a farfasata su fasu da kyau
 2. Sannan a zuba albasa, attaruhu, tafarnuwa, sinadarin dandano, curry, thyme da nama a juya a hankali
 3. A samu dan faranti a ringa diban dankalin ana cura kamar ball ana ajiye
A tsoma wannan ball cikin kwai sai a saka shi cikin bread crumbs a juya sai a saka cikin mai me zafi idan ya soyu a kwashe. Bon apetite.

Domin sanin yadda ake donut danna nan

labarin da yawuceYadda AkeTherapeutic Food (abincin yara)
Labarin na GabaYadda Ake Haɗa Groundnut, Rice, Sweet Potato Shake