Yadda AkeTherapeutic Food (abincin yara)

0
1674

Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abinci, namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a saukake, tare da ni Hafsat Shettimah. A yau za mu koyar da yadda ake Abincin yara (therapeutic food) ku biyo ni a sannu domin mu koya  tare.

Ko kun san yara masu cutar yunwa (tamowa) idan ana ba su wannan zai ƙara musu kuzari da kumari a jikinsu?

Abubuwan Buƙata

 1. Gyaɗa (kofi biyu)
 2. Waken suya (kofi biyu)
 3. Dawa (kofi shida)
 4. Siga
 5. Madara (in ana buƙata).

Yadda ake haɗawa

 1. A soya gyaɗa a bushe ta, sannan a niƙa
 2. A soya waken (soya beans) shi ma a niƙa
 3. Dawa ita ma a soya ta, sannan a niƙa
 4. Cikin roba mai kyau a haɗa dukkanin garin (wake soya, dawa da kuma gyaɗa ) a juya da kyau sai a sami leda mai kyau a juye a cikin sannan a saka a roba mai murfi a rufe. Duk sanda za a yi sai a ɗiba.

Yadda ake haɗa kunun.

 • A ɗora tukunya mai zurfi, sannan a zuba ruwan zafi kaɗan yadda zai isa (kamar talge).
 • A ɗan kofi ko roba, a ɗebi garin kunun yara sai a zuba ruwa a cikin ɗan kadan a dama.
 • Idan ruwan ya tausa (tafasa) sai a zuba wannan gasarar kunun a cikin ruwan, a yi ta juyawa har sai ya yi kauri
 • Za’a iya saka madara domin ƙarin daɗi kuma za a iya sha a haka.

Domin Yadda Ake Gasarar Gyada (Peanut Butter) danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Yin Ƙuli-ƙuli
Labarin na GabaYadda Ake Groundnut Sweet Potato Balls