Yadda Ake Miyar Kayan Ciki

0
660

Miyar kayan ciki wadda aka fi sani da pepper soup; Wannan miya ana haɗa ta ne da kayan ciki kamar su hanji, hanta da dai sauransu.

Abubuwan Da Ake Buƙata Idan Za A Haɗa Miyar su ne:

 • Tumbi
 • Kitse
 • Hanta
 • Zuciya – huɗu
 • Albasa
 • Salt & maggi (abin ɗanɗano da gishiri)
 • Markaɗe
 • Tafarnuwa
 • Masoro
 • Girfa
 • Habbahan

Kayan Aiki

 • Murhu/Risho/Gas
 • Tukunya
 • Mazubi (mai tsafta)
 • Cokali
 • Abin daka
 • Wuƙa

Yadda Ake Haɗawa

A sami tumbi da kitse da hanta da zuciya da huhu da kuma hanji, sai a sami ruwa a tafasa a ɗauko hanjin, sai a samu mutum biyu, ɗaya ya riƙe ɗayan gefen.

Sai a tsoma shi cikin ruwan zafi sai a sa wuƙa a kankare shi, sai ya yi haske, sai a yayyanka ƙanana, sai a wanke hanjin sosai a tabbatar ya wanku a tsane

Sannan a sa albasa da mai da gishiri da kuma maggi, za a ga ya yi ruwa, sai a sa markaɗe irin na farko, in ruwan ya yi kaɗan a ɗan ƙara a bar shi ya yi ɗan kauri 

Daga ƙarshe, a ɗauko tafarnuwa a daka da masoro a jefa girfa a ciki da habbahan a juya in ta yi a sauke

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Miyar Agushi danna nan

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Haɗaɗɗiyar Miyar Gyaɗa. danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Kufta
Labarin na GabaYadda Ake Fish Cake