Yadda Ake Miyar Alaiyahu Domin Ƙarin Lafiya

0
3420

Barkan mu da sake kasancewa a fannin girke-girken WikiHausa. A yau za mu koyar da yadda ake miyar alaiyahu, kuma wannan miyar, za ki iya cin abubuwa da yawa da ita.

Alaiyahu yana ɗaya daga cikin nau’in ganyayyaki girki, mai amfani da kuma lafiya a jikin ɗan Adam. yana da saurin narkewa a ciki kuma mai yawan cinsa yana hana kitse zama a ciki da kuma daidaituwar ƙiba a jiki.

Abubuwan da ake buƙata
 1. Manja
 2. Albasa mai lawashi
 3. Kayan miya
 4. Naman rago
 5. Allayahu
 6. Kayan ɗanɗano
 7. Tafarnuwa
 8. Kayan ƙamshi
Yadda ake haɗawa
 • Ki tafasa namanki tare da albasa, ki sanya kayan ɗanɗano.
 • Ki zuba manja a cikin tukunyar, sai ki yanka albasa, ki zuba naman ya soyu sama-sama, sannan ki zuba kayan miyan da ki ka niƙa.
 • Ki yi ta jujjuya shi, har sai ya soyu, saboda kar ya kama ƙasan tukunya, sannan ki zuba wannan ruwan tafashen naman a ciki.
 • Ki zuba kayan ɗanɗano. Sai ki yanka allayahu, Ki zuba allayahu ki juya idan ta dahu sai a sauke.
Domin koyan Yadda ake dafa miyar agushi danna wannan koren rubutun.

 

labarin da ya wuceYadda Ake Samosa A Sauƙaƙe
Labarin na GabaJinin Haila (Jinin Al’ada)
Khadija Yusha'u (Amira)
Khadija Yusha'u (Amira) Babbar ɗalibar Addini ce, wacce ta karanci abin ci da lafiyar sa (Food and Nutrition) da kuma ƙwararriyar mai haɗa abin ci da kuma koyar da aikin hannu.