Yadda Ake Shinkafa Da Miyar Attaruhu

0
3260

Shinkafa Da Miyar Attaruhu: Shinkafa da miyar attaruhu abinci ne da aka fi yawan cin sa da rana; musamman saboda gina jiki da kuma samar da kuzari…

Kayan Haɗi:

1. Shinkafa
2. Attaruhu
3. Albasa
4. Koren tattasai
5. Ƙwai
6. Plantain
7. Mangyaɗa

Yadda Ake Haɗawa

Da farko uwar gida za ki ɗora ruwa a wuta, idan ya tafasa sai ki zuba shinkafa. Idan ta yi rabin dahuwa, sai ki sauke ki wanke ta; ki tace ki mayar tukunya, kisa ruwa kaɗan yadda zai turara ta; amma fa kar ya yi yawa don ba a son shinkafar ta caɓe, sai ki rage wuta.

Sai ki ɗauko attaruhu ki wanke ki jajjaga, sai ki sa albasa ita ma a yanka ta, yankan tsaye ki wanke ta; ki bar ta a kwando ta tsane, sannan ki ɗauko koren tattasai, ki yanka shi, ki ajiye a gefe.

Sai ki ɗauko plantain ki ɓare, ki yanka ta, sai ki koma kan shinkafarki; idan ta turara sai ki sauke ki bar ta a tukunyar ta ɗan sha iska, kafin ki zuba a plaks,

Sai ki ɗauko kasko ko tukunya ki zuba mai ki soya plantain ɗin nan ki ajiye a gefe. Sannan ki ɗauko tukunyar da za ki yi miyarki a ciki, ki zuba mai; idan ya yi zafi, sai ki sa albasa idan ta yi brown, sai ki zuba attaruhun da kika jajjaga da albasa da koren tattasan. Sai ki juya za ki iya sa farin maggi kaɗan idan kina so,

Sai ki sa maggi mai star da sauran kalolin maggin da kike so, ki sa seasoning mai daɗi, sai ki zuba citta da kanunfari kadan; wanda dama already ana so mace ta dake citta, kanunfari, masoro, gyaɗar Yarbawa mai ƙamshi da tafurnuwa ta dake abinta, ta zuba a roba idan za ki yi jar miya ko jallop sai ki saka.

To bayan kin zuba sai ki juya sosai, idan miyar ta soyu, sai ki rufe ki rage wutar ki bar shi zuwa minti ɗaya, da kin bude za ki ga miyar ta kwanta, kayan miyan sun haɗe jikinsu. Sai ki sauke ki ɗora ruwa, ki dafa ƙwai idan ya huce, sai ki ɓare shi, ki kwashe shinkafarki, sai ki zuba a plet; sai ki sa miyar a gefe ki zuba plantain ɗinma a gefe, sannan ki sa ƙwanki a gefe; ki ɗanyi musu decoration mai kyau. Shi kenan girkinki ya kammala sai ci.

Domin karanta yadda ake Yadda Ake Shinkafa ‘Yar Senegal ko Yadda Ake Yin Alalan Shinkafa danna nan.

labarin da ya wuceHanyoyi 11 Da Ake Rage Ƙiba Ba Tare Da An Kashe Ko Sisi Ba.
Labarin na GabaYadda Ake Miyar Agushi
Khadija Yusha'u (Amira)
Khadija Yusha'u (Amira) Babbar ɗalibar Addini ce, wacce ta karanci abin ci da lafiyar sa (Food and Nutrition) da kuma ƙwararriyar mai haɗa abin ci da kuma koyar da aikin hannu.