Yadda Ake Pizza

0
2457

Pizza abin maƙwalashe ne da ake yin sa da fulawa da wasu abubuwa na amfanin yau da kullum. Ana cin shi da shayi ko da lemo.

Abubuwan Da Ake Buƙata

· Fulawa
· Gishiri
· Yis
· Olive oil (man zaitun)
· Cheese Man shanun kanti
· Mayonnaise
· Kayan ƙamshi
· Tumatir, albasa, koren tattasai
· Tsokar kaza

Yadda Ake Haɗawa

 1. Da farko za a jika yis da ruwan ɗumi, kamar tsawon minti 10, sai ki zuba gishiri da man zaitun.
 2. Sannan sai ki ƙara fulawa a cikin wannan ruwan yis ɗin, ki kwaɓa har sai ya yi tauri.
 3. Idan ma kika ji shi ya yi ruwa ko laushi sosai, sai ki ƙara fulawa don ya yi tauri.
 4. Daga nan sai ki rufe ki bar shi ya hau zuwa mintina 30.
 5. Idan ya hau (kumbura), sai ki sami farantin gashi, ki juye fulawar a ciki, sannan ki sanya a cikin oven, ki gasa ki bar shi tsawon mintuna biyar.
 6. daga nan, sai ki yanka tumatir da farar albasa da koren tattasai ƙanana. Sai ki koma wurin fulawarki, ki duba idan ta gasu, sai ki fito da ita.
 7. Ki ɗauko kayan tumatir ɗin da kika yanka, sai ki zuzzuba a kai da ɗan garin kayan ƙamshi, ki barbaɓa.
 8. A sami tsokar naman kazarki, da kika yanka ƙanana, tare ki zuzzuba a kai. Sannan sai ki kawo mayonnaise ki yaryaɗa a kai.
 9. Sai ki zo ki rufe samansa da manshanun kanti (chease).
 10.  ki Mayar cikin abin gashin (oben) don ya kara gasuwa.
 11. Za ki ji yana ƙamshi sosai, sai ki fito da shi daga ciki, shi ke nan Pizza ta yi sai ci.

Domin karanta Yadda Ake Mini Pizza ko Yadda Ake Dafaffiyar Gyaɗa dannan nan.

labarin da ya wuceWane Ne Ya Raɗa Wa Manzon Allah(S.A.W) Suna Muhammad?
Labarin na GabaWaɗanda Allah Ke Gaggauta Karɓar Addu’ar Su