Yadda Ake Haɗin Yaji

0
1985

Barkan mu da sake kasancewa cikin shirinmu na girka-girken WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Nijeriya da na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu a jikin ɗan Adam cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shettimah. A Yau za mu koyar da yadda ake Haɗin yaji na musamman, ku biyo ni domin mu koya tare.

Yadda ake Haɗin Yaji Na Musamman

Abubuwan da ake buƙata

Barkono
Citta
Kanumfari
Masoro
Kirfa (Cinnamon)
Tafarnuwa

Gyadar miya (Nutmeg)
Ƙuli-ƙuli
Sinadarin Ɗanɗano

Yadda Ake Haɗawa

1. A gyara komai a fitar da datti.
2. A daka komai daban-daban, a tankaɗe su, sai a haɗe su, a zuba sinadarin ɗanɗano a ƙara dakawa har su hade jikinsu.
3. A adana yaji a mazubi mai kyau, mai murfi.

Domin sanin yadda ake dambun nama danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Dambun Nama
Labarin na GabaManufar Rayuwar Aure A Addini Da Wayewar Zamani