Manufar Rayuwar Aure A Addini Da Wayewar Zamani

0
263

MANUFAR RAYUWAR AURE A ADDINI DA WAYEWAR ZAMANI.

Rayuwa ba manufa, rayuwa ce marar dandano. Matukar ma’aurata sun hadu akan manufa daya zasu rayu ne akan wannan manufar, amma in akayi rashin dace yadda miji yake kallon al’amura da banbanci da nahiyar da ita take kallo, toh! anan tushen sabani yake. In dai manufa kuwa zata banbanta hanyoyin isa ga manufar ma zasu banbanta. A wannan yanayi sabani da cin karo zai dabaibaye zamantakewar aure, saboda ba akan manufa daya ake tafiya ba. duk kammalallen mutum ya na samun nasara ne saboda dabiar tsayuwa akan manufa. A cikin manufar samar da dan adam zamu iya fahimtar gamammiyar manufar aure.

Ma’aurata ku sani manufarku ta farko ta kasance zaman ibada da neman yardar Allah ba al’ada ba. Akwai kebantacciyar manufar aure nau’ika biyu; Asliyyah; Kiyaye wanzuwar jinsin dan adam. Sai kuma Taba’iyya sauran manufofi da mutum ya kudura a ransa a matsayin manufar da ta motsa shi ya yi aure;haihuwa, kamewa daga sha’awa,biyan bukatar dabi’a, godewa ni’imar Allah, rayuwar taimakekeniya, sanyaya zuciya da debe kewa da ma kyakkyawar manufa ta al’adun mutane tsaftattu.

Ma’auratan da suka gina zamantakewar aurensu akan manufa ingantacciya sun fi kusa da jin tsoron Allah wajen kulawa da hakkokin junansu, kuma aure yafi albarka.

Duba:
1. Al-Maqaasidul aammah lis shari’atil Islamiyyah na Dr. Yusuf Hamid al-Aalim sh393

2. The 5 love languages; The secret of love that lasts na Gary Chapman.

Domin sanin yadda mutun yake da ruhi ba da jiki a danna nan