Yadda Ake Miyar Karkashi Da Kuɓewa

0
1174

A yau za mu koyi Yadda Ake Miyar Karkashi Da Kubewa

Miyar karkashi da kuɓewa na da matukar daɗi da kuma amfani a jikin ɗan Adam, tana da matukar amfani musamman ma a wajen masu ciwon suga da kuma ƙarin jini ga marasa jini wato (anemic patients) dama wasu amfanin da dama. Yana da kyau a ƙalla ko sau ɗaya a sati mutum ya ci ta, amma idan ya tabbatar ya cika ta da nama

Abubuwan da ake buƙata

 • Ganyen karkashi
 • Kuɓewa ɗanya
 • Tokar miya ko kanwa
 • Attaruhu
 • Bandar kifi
 • Nama
 • Albasa
 • Ɗanyar tafarnuwa
 • Garin citta
 • Magi

Yadda ake haɗawa

 1. A kakkabe ganyen karkashin tsaf, sannan a yayyanka shi ƙanana sosai.
 2. A samu kuɓewa ɗanya, a yayyanka ta, sannan a saka a turmi a daka ta, ta yi laushi sosai.
 3. In kuma da kanwa za a yi miyar, sai a daka tare da kanwa kaɗan.
 4. Sannan a kwashe a ajiye a gefe, A daka attaruhu da tafarnuwa sannan a kwashe.
 5. A wanke bandar kifi da ruwan ɗumi, a cire ƙayoyin sannan a yayyanka albasa ƙanana.
 6. A ɗaura ruwa a tukunya sannan a tafasa nama har sai ya yi laushi.
 7. Sai a kara ruwa kaɗan a kan romon naman, sannan a zuba yankakkiyar albasar da jajjagaggen attaruhu da garin citta da bandar kifi har sai sun tafasa. Sannan a ɗauko kubewar da aka daka a zuba a riƙa gaurayawa har sai ta fara nuna.
 8. Sannan a ɗauki karkashin a zuba a dauki maburgi a buga, sannan a cigaba da juyawa.
 9. Idan har ba a sanya kanwa a miyar ba, a wannan lokacin ya kamata a sanya tokar miyar sannan a jiƙa magi ya narke, a zuba sai a cigaba da gaurayawa har sai ɗanɗanon ya fito sannan a sauke.
Za a iya cin wannan miyar da tuwon semo.
Domin sanin yadda shinkafa yar senegal danna nan