Yadda Ake Moi-Moi Na Musamman

0
518

Abubuwan da ake  buƙata

 1. Wake
 2. Taruhu da tattasai
 3. Albasa
 4. Maggi
 5. Tafarnuwa
 6. Manja
 7. Sausage
 8. Kwai
 9. Karas

Yadda ake haɗawa

 1. Da farko za ki wanke wake a surfa, sai a zuba taruhu da tattasai da albasa a niƙa shi ya yi laushi sosai.
 2. Sannan a zuba wannan haɗin a cikin bowl a sa manja, maggi, tafarnuwa, da curry, za a iya saka cray fish ma, a juya shi sosai komai ya haɗe.
 3. A saka mai kaɗan a kan kaskon, a sa sausage da karas a yi stir frying nasu, sai a sauke. a dafa ƙwai a ɓare shi a yanka slices. Shi ma a aje a gefe.
 4. Za a kunna oven 180° sai a ɗauko parchment paper a shimfiɗa ta a kan faranti na gashi, a zuba ƙullun a saka a oven.
 5. Bayan mintina 10 in ya fara yi, sai a sauko da shi a zuba fillings ko’ina, a mayar ya gama gasuwa.
 6. Idan ya yi, za a ji ƙamshin ya hade ko’ina a sa toothpick a duba,
 7. don a tabbatar ya dahu, a sauke a nade kaman nadin tabarma.

A ɗan bari ya huce sai ki yanka. A ci lafiya

Domin sanin yadda ake zobo na cucumba dannan nan.

labarin da ya wuceYadda Ake Zoɓo Mai Cucumber
Labarin na GabaYadda Ake Cabbage Saurce
Khadija Yusha'u (Amira) Babbar ɗalibar Addini ce, wacce ta karanci abin ci da lafiyar sa (Food and Nutrition) da kuma ƙwararriyar mai haɗa abin ci da kuma koyar da aikin hannu.