Zobo na ɗaya daga cikin abin sha wanda ke taimakawa wajen narkar da abinci, sauko da hawan jini musamman ma idan aka haɗa shi da cucumber.
Kayan da ake buƙata
- Zoɓo
- Cucumber
- Bakin flavour
- Kanunfari
- Citta
- Kimba
- Sugar
Yadda ake haɗawa
- A wanke zoɓon, sai a zuba ruwa a ɗora a wuta
- A zuba su cittar a gurza cucumber a zuba a ciki sai sun dahu sosai
- Sai ki sauke a tace, a zuba flavour masu daɗi da daɗin ƙamshi, in an ji zaƙin ya yi, to ba sai an zuba suga ba.
- In kuma akwai bukatar a zuba, sai a zuba, sai a juya sosai, sai a ɗan ƙara ruwa daidai yadda ake so,
- A saka ƙanƙara a frige, sai a samu kofi mai ƙayatarwa a zuba.
A sha lafiya.
Domin karanta Yadda Ake Haɗa Lemon Tsamiya danna koren rubutu