Garin Kunun Aya

0
64

Ummulkhair Sani Panisau

A yau za mu koyi yadda ake yin Garin Kunun Aya. Kunun Aya kamar yadda muka sani kunun aya yana da matuƙar amfani ga lafiyar mu musamman ma ma’aurata.

Abubuwan da ake buƙata:

Aya.
Dabino.
Kwakwa.
Citta.
kanumfari.

Yadda ake haɗawa:-

A tsinci aya a cire dattin ciki. Ki soya ayar sama-sama yadda za ki ji daɗin niƙawa ya koma gari don kar ya yi saurin lallacewa.

Ki samu kwakwarki (dry coconut) da dabino ki zuba a cikin ayar nan. Sai ki daka cittarki da kanumfari ba da yawa ba saboda kar yawanshi ya ɓata miki ɗanɗanon garin yayi yawa ɗan daidai za ki zuba ki kai a niƙa miki. Bayan nan kafin ki yi packaging ɗinsa ki baza ya sha iska sannan ki saka a cikin mazubinki saboda kar ya sha iska sosai.

Danna nan don karanta Wainar Semovita

Edita:@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceBiyayya Ga Mahaifa (Iyaye)
Labarin na GabaFalalar Salati Ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam)