Abinsha Yadda Ake Zoɓo A Cikin Sauƙi Sabon Salo Daga BHM Ninja - 18/12/2019 0 1659 Yadda ake zoɓo a cikin sauƙi sabon salo. Abubuwan haɗawa 1. Zoɓo 2. Kanunfari 3. kimba 4. Masoro 5. Lemon grass 6. Sugar 7. Ruwa Yadda ake haɗawa 1. Da farko za ki wanke zoɓonki ki sa a tukunya, ki sa ruwa, kanunfari, kimba, masoro, lemon grass ki rufe ki bari ya tafasa sosai sai ki sauke ya huce. 2. Sai ki tace ki sa sikari. Ki sa a firji in ya yi sanyi sai a sha. KU KARANTA Yadda ake lemun abarba a saukake