Yadda Ake Madarar Youghurt

0
1059

Yadda Ake Madarar Youghurt

Abubawan da ake bukata

  • Madara kofi huɗu
  • Ruwa kofi huɗu
  • Sukari kofi
  • Flavor mai ƙamshin madara cikin cokali.
  • Corn starch kofi ɗaya
  • Culture rabin cokali

Yadda ake hadawa:

  1. Da farko za a kwaɓa madarar (ta gari) da sukari da corn starch sai a zuba ruwan sanyi a kai.
  2. Daga nan sai a tafasa ruwan zafi a zuba a kai, idan an ɗan daɗe sai a juya shi, har sai an tabbatar babu ƙulalai ko kaɗan a ciki.
  3. A murje haɗin ya zama ruwa, sannan a bar shi ya huce ya zama da ɗumi.
  4. Kafin ya yi sanyi sosai, sai a zuba culture a ciki.
  5. Bayan an sa culture, sai a rufe a bari ya yi awa takwas zuwa 12, ko ma ya kwana.
  6. Idan aka buɗe shi, sai a zuba sukari da flavor sai a motsa.
  7. Idan yogurt din ya haɗu sai a sa a fridge a bar shi ya yi sanyi.
  8. Daga nan sai a sha shi yadda ake so.

Karin haske:

Za a iya amfanin da madarar gari ko ta ruwa wajen haɗa yogurt na gida.
Idan da madarar gari za a yi amfani, to yadda na yi bayani haka za a yi.
Idan kuma da madarar ruwa ce, to a dafa madarar sannan a ɗiga mata culture, a rufe na tsawon awa takwas koh sha biyu.
Wannan shi ne yadda ake yin yogurt a gida daki-daki.
Za ku kuma iya sha da fura ko a kankare kwakwa a ciki yogurt din a sha
labarin da ya wuceYadda Ake Gas Meat
Labarin na GabaYadda Ake Ajiye Kayan Miya Tsawon Shekara
Khadija Yusha'u (Amira)
Khadija Yusha'u (Amira) Babbar ɗalibar Addini ce, wacce ta karanci abin ci da lafiyar sa (Food and Nutrition) da kuma ƙwararriyar mai haɗa abin ci da kuma koyar da aikin hannu.