Yadda Ake Gas Meat

0
892

A yau za mu koyi yadda ake gas meat.

Abubuwan Da Ake Buƙata:

  • Jan nama
  • Albasa ko lawashi
  • MarkaÉ—aÉ—É—iyar gyaÉ—a
  • Kori
  • Thyme
  • Tattara
  • Attaruhu
  • Tumatur kaÉ—an
  • Maggi
  • Kabeji
  • Tafarnuwa
  • Foil paper ko takardan cementi
  • Da leda baÆ™i

Yadda Ake HaÉ—awa

  1. A wanke nama.
  2. A yanka albasa ko lawashi.
  3. A jajjaga tattara da attaruhu.
  4. A yayyanka tumatur.
  5. A haɗa nama, albasa, da kayan miya, da gyaɗa, kori, thyme, maggi da sauran kayan ƙamshi a gauraya, idan ana so a sa tumatur ko kuma a bar shi sai bayan kori ya nuna a zuba shi ɗanye a kan naman a ci.
  6. A juye haÉ—in baki É—aya a cikin foil paper a kunshe ko kuma a leda, sai a sa ledar a cikin takarda, takardan kuwa a cikin wani leda.
  7. A ɗora tukunya da ruwa, idan ya yi zafi ko ya tafasa a dora matsami kamar za a yi dahuwar dambu, a dora ƙunshi a kai a rufe da marfin tukunya a bari ya nuna.
  8. Idan ya nuna za a iya garnishing da cabbage, tumatur, koren tatttasai a ci.
  9. Za a iya kuma amfani da oven in da hali ba dole sai tukunya ba.

Domin sanin Yadda Ake Stuffed Meat danna nan