Yadda Ake Kek Ɗin Gyada (Groundnut Cake)

0
1371

Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe, tare da ni Hafsat Shettimah. A yau za mu koyar da yadda ake kek ɗin gyaɗa (Groundnut Cake). Ku biyo ni a sannu domin mu koya tare……

Ko kun san gyaɗa tana ɗauke da sinadarai irin su vitamin E, zinc da kuma magnesium wanda yake taimako wajen gyara fata.

Abubuwan Da Ake Buƙata

 1. Soyayyar gyada.
 2. Fulawa kofi ɗaya
 3. Fulawar gyada ¼ cup
 4. Siga ½ kofi
 5. Bota ¼ kofi
 6. ƙwai 4
 7. Flavour 1 teaspoon
 8. Baƙin hoda (Baking powder) 1 teaspoon
 9. Madara ½ kofi.

Yadda Ake Haɗawa

 1. A buga bota da siga da kyau, har sai aukin botar ya ninku.
 2. Sai a zuba filabo (flavour), ƙwai da madara, a sake buga su sosai.
 3. Sannnan a zuba flour da baking powder, sai a buga shi kamar na minti uku zuwa huɗu sai a zuba marmashasshiyar gyaɗa a juya.
 4. A shafa wa gwangwanin cake bota, sai a barbaɗa fulawa.
 5. A zuba kwaɓin cake a cikin gwangwanin, sai a ɗauko crushed gyaɗa a barbaɗa a saman kwaɓin
 6. A saka cake a cikin abin gashi kamar na minti 15 ko idan an zura tsinke ya fito babu ƙullin kek a jiki.

Domin sanin Yadda Ake Kunun Gyaɗa danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Kunun Gyaɗa Mai Gasara
Labarin na GabaYadda Ake Biredin Gyaɗa (Groundnut Bread)
Sunana Buhari Ibrahim Aliyu [Googler] dalibin computer, digital marketer, technical crew a wikihausa dalibi mai kokarin yada ilimi na na'aura mai kwakwalwa tare da tabbatar cigaban kasuwancin zamani.